Wani jigon jam’iyyar APC ya gamu da ajalinsa a hannun yan bindiga a Abuja

Wani jigon jam’iyyar APC ya gamu da ajalinsa a hannun yan bindiga a Abuja

Wasu gungun yan bindiga sun aikata aika aika akan wani jigon jam’iyyar APC, kuma shugaban jam’iyyar APC a mazabar Dobi cikin karamar hukumar Gwagwalada, Alhaji Hussani Sarki Kaida, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun kashe Hussaini ne a ranar Asabar 26 ga watan Janairu da misalin karfe 1:20 na dare a gidansa dake kauyan Kaida, sa’annan suka yi awon gaba da diyarsa yar shekara goma sha biyar, Saude.

KU KARANTA: El-Rufai ya fallasa tuggun da PDP ke shiryawa na tayar da hankali a zaben 2019

Wani dan uwan Hussaini, Ibrahim Sarki, ya bayyana cewa miyagun mutanen sun kutsa kai cikin gidan Hussaini dauke da muggan makamai ne, inda suka kwankwasa masa kofa, bude kofarsa keda wuya suka dirka masa harsashi.

“Karar harbin da suka yi masa na ji, ko kafin na Ankara da abinda ke faruwa sai ganin gawarsa muka yi a kasa kwance cikin jini, a kirji suka harbeshi, kuma nan take ya mutu. Daga nan ne kuma suka yi awon gaa da diyarsa Saude, shekarunta 15.” Inji shi.

Malam Ibrahim yace tuni sun binne marigayi Hussaini kamar yadda dokokin addinin Musulunci suka tanadar, a kauyensu na Kaida, sa’annan yace har yanzu basu ji daga bakin miyagun game da halin da diyarsa Saude take ciki ba.

Ba wannan bane karo na farko da ibtila’I ke fada ma Hussaini ba, inda ko a kwanakin baya sai da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da shi, har sai daya biya kudin fansa na naira miliyan biyu sa’annan suka sakeshi.

Shima shugaban karamar hukumar Gwagwalada, Adamu Mustapha ya bayyana kaduwarsa gami da bakin ciki game da yadda aka kashe marigayi Hussaini, inda yace yana mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da jama’an Gwagwalada gaba daya.

Daga karshe shugaba Mustapha yayi kira ga hukumomin tsaro dasu tabbata sun kama duk masu hannu cikin kisan marigayi Hussaini, tare da tabbatar da ganin sun fuskanci hukuncin daya dace dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel