Yiwa jam'iyya zagon kasa: An tsige Okorocha a matsayin jagorar yakin neman zabe

Yiwa jam'iyya zagon kasa: An tsige Okorocha a matsayin jagorar yakin neman zabe

- An tsige Gwamna Rochas Okorocha a matsayin jagoran yakin neman zaben APC a jihar Imo

- Wannan ya biyo bayan hukuncin da kwamitin ladabtarwa na jihar ta yanke ne a kansa saboda zagon kasa da ya ke yiwa jam'iyyar

- Okorocha dai ya lashi takobin yiwa surukinsa da ke jam'iyyar jam'iyyar Action Alliance, Uche Nwosu kamfen a maimakon dan takarar APC, Hope Uzodinma

Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar All Progressives Congress APC reshen jihar Imo ta tsige gwamnan jihar Rochas Okorocha a matsayin jagoran kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar a jihar.

Wannan ya biyo bayan umurnin da kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar taq bayar ne bayan gudanar da bincike a kan zargin yiwa jam'iyyar zagon kasa da ake zargin gwamnan da wasu 'yan jam'iyyar da aikatawa.

Kwamitin da aka nada karkashin Mathew Omegara ta gayyaci gwamnan da wasu mutane shida a jihar su gurfana a gaban ta.

DUBA WANNAN: Jirgin kasa: Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari

An tsige Okoroha a matsayin jagorar yakin neman zabe

An tsige Okoroha a matsayin jagorar yakin neman zabe
Source: UGC

Sakataren APC na kasa, Mallam Lanre Issa-Onilu ya ce kwamitin gudanarwa na jam'iyyar zai zauna domin duba shawarar da APC na jihar Imo ta bayar na dakatar da Okoroha.

"Abinda ya faru a Imo ya nuna cewar APC ba wasa ta keyi da kowa ba. Idan dai sun bi dokoki babu wata matsala da za a samu. Idan suka gabatar mana da shawarwarin su, zamu duba," inji shi.

Sai dai wani mamban jam'iyyar APC reshen jihar Imo ya sanar da majiyar Legit.ng a ranar Lahadi cewa jam'iyyar ta riga ta dakatar da Okorocha a matsayin jagoran kwamitin yakin neman zabe a jihar.

Okorocha ya lashi takobin yiwa surukinsa da ke jam'iyyar Action Alliance, Uche Nwosu kamfen duk da cewa APC tana da dan takarar ta Sanata Hope Uzodinma.

Majiyar ta ce: "Tuni jam'iyyar APC ta tsige Okorocha a matsayin jagoran kwamitin yakin neman zabe, ta umurci Uzodinma ya maye gurbinsa. A yayin da mai dakin shugaban kasa ta ziyarci Imo domin yakin neman zabe, gwamnan ya gayyaci surukinsa kuma ya daga hannunsa. Wannnan abin ya bamu mamaki kuma munyi masa kallon cin fuska da mai dakin shugaban kasar da jam'iyyar."

Da aka tuntubi mai magana da yawun APC, Issa-Onilu domin samun karin bayani a kan lamarin, ya ce tuni an dakatar da Okorocha saboda bukatar hakan ya fito ne daga mazabarsa.

Ya ce wannan na nufin Okorocha ba zai iya cigaba da aiki a matsayin jagoran kwamitin yakin neman zabe a jiharsa ba.

Issa-Onilu ya ce, "Jam'iyyar APC ta umurci gwamnonin ta su jagoranci yakin neman zaben jihohinsu. Amma a jihohin da ba bu gwamnoni, 'yan takarar gwamnan ne za su jagoranci yakin neman zaben. Tunda Okorocha ya juya wa jam'iyyarsa baya, ba bu yadda za ayi ya cigaba da jagorancin yakin neman zaben."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel