Dakatar da CJN: Buhari ya gayyaci sanatocin APC taro a fadar Aso Rock

Dakatar da CJN: Buhari ya gayyaci sanatocin APC taro a fadar Aso Rock

Shugaba Muhammadu Buhari ya gayyaci sanatocin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ke majalisar dattawa zuwa wani taro a fadarsa saboda dakatar da alkalin alkalai na kasa, Jutice Walter Onnoghen.

Shugaba Buhari ya dakatar da Onnoghen ne a ranar Juma'a a bisa shawarar kotun da'ar ma'aikata CCT.

An maka shi ne a CCT inda ake tuhumarsa da aikata laifuka shida masu alaka da rashin bayyana kadarorinsa.

Shugaban kasar zai gana da sanatocin na APC ne gabanin taron gaggawa da za su gudanar a majalisar dattawa a gobe (Talata) domin daukan mataki a kan dakatar da Onnoghen da shugaban kasar ya yi.

Dakatar da CJN: Buhari ya gayyaci sanatocin APC taro a fadar Aso Rock

Dakatar da CJN: Buhari ya gayyaci sanatocin APC taro a fadar Aso Rock
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Jigo a jam'iyyar APC ya fadi su waye ke tsoron tazarcen Buhari

A taron, ana sa ran sanatocin na APC za su dauki mataki ne a kan dakatar da Onnoghen da mambobin jam'iyyun adawa suka rika suka.

Sai dai anyi yiwa taron lakabi ne da liyafar cin abinci da za a gudanar a banquet Hall kamar yadda takardar gayyatar da ke dauke da sa hannun Direkta Janar na Kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa, kuma Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya sanya hannu a kai.

Wani na kusa da wadanda ke shirya taron sun ce shugabanin jam'iyyar APC suma za su hallarci taron.

Ya kara da cewa baya ga shugabanin APC, an gayyaci wasu gwamnonin jam'iyyar zuwa wurin taron.

Ya ce, "Ka san shugabanin majalisa 'yan jam'iyyar adawa na PDP ne kuma jam'iyyar ta bayyana matsayan ta a kan dakatar da alkalin alkalai na kasar.

"Kazalika, shugaban majalisar dattawa wanda kuma shine Direkta Janar na yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasa na PDP, Bukola Saraki shima ya bayyana matsayarsa a kan wannan batun.

"Saboda haka yana da muhimmanci mu tattauwa da 'yan jam'iyyar mu domin ganin ba su bari Saraki ya kakkaba musu ra'ayinsa ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel