El-Rufai ya fallasa tuggun da PDP ke shiryawa na tayar da hankali a zaben 2019

El-Rufai ya fallasa tuggun da PDP ke shiryawa na tayar da hankali a zaben 2019

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya zargi jam’iyyar PDP da shirya wasu tuggu domin tayar da hankali a yayin babban zaben shekarar 2019, saboda a cewarsa PDP ta hango cewar ba zata kai labari a zaben ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Kudan ta jahar Kaduna, inda yace sun samu wannan bayani ne daga majiyoyi masu karfi, don haka tuni suka umarci hukumomin tsaro dasu tabbata sun dakile wannan yunkuri.

KU KARANTA: Rundunar Soji ta tura gwarazan yan mata filin daga domin fafatawa da Boko Haram

El-Rufai yace a shirye hukumomin tsaro dake jahar Kaduna suke domin tabbatar da sun kama duk wani mai hannu cikin yunkurin tayar da zauni tsaye tare da kawo cikas ga zaman lafiyan da ake samu a jahar.

“A matsayina na shugaba, hakkinku ne na bayyana muku abubuwan dake faruwa, saboda akwai manyan yayan jam’iyyar PDP a karamar hukumar Kudan, kuma zasu yi kokarin tayar da hankali a garin nan.

“Don haka a duk lokacin da wani dan siyasa ya nemi ku tayar da hankali, ku fada masa ya kawo yayansu ku yi aikin tare, yan siyasa sun saba amfani da yayan talakawa wajen gudanar da munanan ayyuka, yayin da yayansu ke kasashen waje suna karatu, amma ai rai bai fi rai ba.” Inji shi.

Bugu da kari, El-Rufai ya bayyana cewa siyasa yar ra’ayi ce, inda yace ba’a tilasta ma mutum wanda zai zaba, sai dai a matsayinka na dan siyasa ka bashi hujjar daya kamata ya zabeka, “Ana iya samun yan gida daya su zabi yan takara daga jam’iyyu daban daban.” Inji shi.

Daga karshe gwamnan ya jaddada ma al’ummar Kudan cewa ba wai ya zabi Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyarsa saboda addininta bane, illa kawai don kwarewarta, gogewa da kuma sanin makaman aiki.

Daga cikin manyan siyasan jahar Kaduna da suka fito daga garin Kudan akwai dan takarar gwamnan jahar Kaduna a inuwar jam’iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan, da kuma Sanata Suleiman Othman Hunkuyi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel