Ba mu karbi Biliyan 163 a hannun Gwamnatin Najeriya ba – Inji ASUU

Ba mu karbi Biliyan 163 a hannun Gwamnatin Najeriya ba – Inji ASUU

Mun ji cewa Kungiyar Malaman Jami’a na Najeriya watau ASUU ta musanya cewa sun karbi makudan kudi daga hannun gwamnatin tarayya da nufin janye yajin dogon aikin da su ke ta faman yi.

Ba mu karbi Biliyan 163 a hannun Gwamnatin Najeriya ba – Inji ASUU

Kungiyar ASUU tace shugabannin Jami'o'i ake ba kudi ba ita ba
Source: UGC

Kungiyar ASUU ta maida martani ga labarin da ake ta ji na cewa gwamnatin tarayya ta ba ta Naira Biliyan 163 domin a kawo karshen yajin aikin da ake yi a jami’o’i. ASUU tace bbau gaskiya a wannan labari da ake ta yadawa.

Dr. Ade Adejumo wanda yana cikin manyan jagororin kungiyar ASUU ya bayyana cewa ba su karbi kudin da ake fada daga hannun gwamnati ba. Ade Adejumo yace asali ma dai ASUU ba ta karbar kudi daga hannun gwamnati.

Dr. Adejumo yake cewa shugabanni da hukumomin jami’o’i ne gwamnatin tarayya kan ba kudi ba wai kungiyar ASUU ba. Jagoran kungiyar Malaman makarantar yace babban burin ASUU shi ne ganin an gyara Jami’o’in Najeriya.

KU KARANTA: ASUU na iya komawa cikin ajin karatu kwanan nan – Gwamnatin tarayya

Wannan kusa na kungiyar ASUU da ke Jami’ar tarayya ta Ibadan yace har albashin ‘yan kungiyar su da kuma alawus din su ya kan fito ne ta hannun jami’o’i, don haka a rika yada labari cewa an ba ASUU makudan kudi karya ce kurum.

Yayi kira a na sa bangare ga shugabannin jami’o’i da su dage wajen ganin ASUU ta cin ma burin ta na ganin makarantun na gwamnati su na samun kulawar da ta dace domin inganta harkar ilmi da ke neman tabarbarewa a Najeriya.

A baya dai mun ji cewa gwamnati ta fito tace yajin aikin na ASUU wanda yake neman kai watanni 3 ya kusa zuwa karshe. Sai dai kuma da alamu har yanzu akwai sauran aiki kafin a cin ma yarjejeniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel