Lamari ya girmama: Dan takarar gwamnan APC ya garzaya wajen Dahiru Bauchi neman tabarraki

Lamari ya girmama: Dan takarar gwamnan APC ya garzaya wajen Dahiru Bauchi neman tabarraki

A yayin da ake gab da shiga babban zaben shekarar 2019, yan siyasa da dama sun bazama neman hanyoyi daban daban da suke ganin zasu kaisu ga gaci, tare da basu nasara a zaben, ko ta halin kaka kuwa.

Shima dan takarar gwamnan jahar Gombe a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Inuwa Yahaya ba’a barshi a baya ba, inda ya garzaya gidan fitaccen Malamin darker tijjaniyyah, Shehi Dahiru Usman Bauchi domin neman tabarraki daga malamin.

KU KARANTA: Buhari ya bada umarnin kulle jami’o’I da manyan makarantu 68 na je ka na yi ka

Lamari ya girmama: Dan takarar gwamnan APC ya garzaya wajen Dahiru Bauchi neman tabarraki

Shehi
Source: Facebook

Haka kuwa aka yi, ya yi dace, Shehin Malamin yayi maraba da zuwansa, sa’annan ya yi masa addu’a, daga bisani kuma ya umarceshi ya cire hularsa, ya mika masa kansa, inda Shehu ya kama kan dan takarar gwamnan ya yi masa addu’a, tare da sanya masa tabarraki.

Legit.ng ta ruwaito Inuwa Yahaya ya samu nasarar zama halastaccen dan takarar gwamnan jahar Gombe ne bayan ya lallasa abokan karawarsa su 8 da suka fafata tare a zaben fidda gwani da jam’iyyar APC ta shirya, inda ya samu kuri’u 859.

Lamari ya girmama: Dan takarar gwamnan APC ya garzaya wajen Dahiru Bauchi neman tabarraki

Shehi
Source: UGC

Daga cikin wadanda Inuwa ya kayar akwai tsohon dan majalisar wakilai, tsohon Sanata, kuma tsohon minista a zamanin Goodluck, Umar Idris, wanda ya samu kuri’u 68 kacal, sauran sun hada da Mohamemd Barde, Farouk Bamusa, Umar Kwairanga, Habu Muazu, Dasuki Jalo, Kamisu Mai Lantarki da Aliyu Haidar.

Inuwa wanda shine dan takarar APC a zabe gwamna a shekarar 2015 a yanzu zai fafata ne da tsohon mataimakin kaakakin majalisar wakilai, kuma Sanata mai ci, Bayero Nafada daga jam’iyyar PDP, a takarar gwamnan jahar Gombe da za’a buga a ranar 2 ga watan Maris.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel