Onnoghen: ADC ta neman Bukola Saraki ya dare kan kujerar Buhari

Onnoghen: ADC ta neman Bukola Saraki ya dare kan kujerar Buhari

Mun ji cewa Shugaban jam’iyyar ADC na African Democratic Congress, Cif Ralphs Nwosu, yayi kira ga majalisar tarayya tayi wuf ta nada Bukola Saraki a matsayin shugaban kasar Najeriya da gaggawa.

Onnoghen: ADC ta neman Bukola Saraki ya dare kan kujerar Buhari

Jam’iyyar hamayya tana neman Majalisa ta tsige Shugaba Buhari
Source: UGC

Ralphs Nwosu ya neman shugaban majalisar dattawan kasar yam aye gurbin shugaba Muhammadu Buhari ne a dalilin karon tsayen da shugaban kasar yayi wat sarin mulkin Najeriya wajen dakatar da babban Alkali Walter Onnoghen.

Jam’iyyar ta ADC ta fitar da wannan jawabi ne ta bakin babban Sakataren ta na yada labarai na kasa, Yemi Kolapo. Kolapo ya bayyana cewa ya zama dole a tsige Buhari da Osinbajo ganin yadda su ke cigaba da keta dokar kasar nan.

KU KARANTA: CJN yayi kira ga Alkalai su zama masu gaskiya a gaban shari'a

Jam’iyyar adawar tace gwamnatin Buhari ta aikata babban laifi don haka bai dace a bar shugaban kasar da mataimakin sa, Yemi Osinbajo, su cigaba da mulki ba. Jam’iyyar tace ya kamata majalisa ta sa kai ta karbi ragamar mulkin kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust, ADC tana kukan cewa shugaba Buhari bai da hurumin dakatar da Alkalin Alkalai na kasa baki daya don haka tace taba Walter Onnoghen babban laifi ne wanda ya kai ayi waje da Buhari.

Haka zalika dai mun ji cewa jama’a da dama su na cigaba da huro wuta ga shugaba Buhari ya sauka daga kan mulki saboda dakatar da babban Alkalin kasar da yayi a Ranar Juma’ar nan da ta wuce.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel