Za a dauki matakin karshe game da zaben Ekiti a kotun shari’a zabe

Za a dauki matakin karshe game da zaben Ekiti a kotun shari’a zabe

- Kotu za ta bada hukunci a kan zaben Gwamnan Ekiti da aka yi a baya

- Fayemi yana fuskantar kalubale daga ‘dan takarar PDP da ya sha kasa

- Olusola yace an yi magudi ainun a zaben da Fayemi yayi nasara a APC

Za a dauki matakin karshe game da zaben Ekiti a kotun shari’a zabe

An jima jama'a za su san wanda zai cigaba da mulki a Ekiti
Source: Depositphotos

A yau dinnan ne kotun sauraron karan zaben jihar Ekiti za ta bada hukunci game da zaben da aka yi a kwanaki. Jam’iyyar APC ce tayi nasara a zaben inda ‘dan takarar PDP, Kolapo Olusola yake kalubalantar nasarar Kayode Fayemi na APC.

A Ranar Litinin dinnan ne Alkali mai shari’a zai bada hukunci game da ainihin wanda yayi nasara a zaben Ekiti da aka gudanar a tsakiyan Watan Yuli. Ana zaman shari’ar ne a kotun musamman da ke sauraron korafin a Birnin Abuja.

‘Dan takarar PDP a zaben, Farfesa Kolapo Olusola ya garazaya kotu bayan tsohon gwamna Kayode Fayemi ya tika sa da kasa a zaben. Kolapo Olusola wanda shi ne mataimakin Ayo Fayose a lokacin ya tashi da kuri’u 178,223.

KU KARANTA: An nemi Ganduje an rasa wajen muhawarar ‘yan takarar 2019

Shi kuma Dr. Kayode Fayemi, wanda a lokacin minista ne a cikin gwamnatin Buhari ya samu kuri’u 197, 459 ne a zaben. Sai dai ‘dan takarar PDP yana karar cewa an tafka magudi don haka yake neman kotu ta fitar masa da hakkin sa.

Olusola ya fadawa kotun sauraron koke-koken zabe cewa an yi amfani da kudi wajen sayen kuri’in jama’a, sannan kuma yace APC tayi murdiya wajen soke kuri’un da PDP ta samu tare da kuma satar wasu akwatunan zaben.

Ana sa rai yau jama’an Ekiti za su san hukuncin kotun da ke sauraron shari’ar zaben. Wanda ya sha kasa a wannan kotu yana da damar zuwa har gaban kotun daukaka kara na tarayya idan bai gamsu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel