'Yan bindiga sun yi garkuwa da Mutane 7 a jihar Zamfara

'Yan bindiga sun yi garkuwa da Mutane 7 a jihar Zamfara

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu cewa, a daren jiya na Asabar 'yan bindiga sun kai wani mummunan hari a wani gidan kallon kwallo da ke garin Birnin Magaji a karkashi karamar hukumar ta Birnin Magaji da ke jihar Zamfara.

Yayin aukuwar wannan mummunan hari kamar yadda jaridar Legit.ng ta ruwaito, maharan sun yi awon gaba da kimanin Mutane bakwai su na tsaka cikin nishadi a wani gidan kallon tamola da ke wajen garin Birnin Magaji.

A yayin da Hausawa kan ce mugu ba ya son haske ya sanya maharan kimanin su 20 rike da bindigu su ka kai farmaki gidan kallon kwallon da misalin karfe 10 na dare inda suka ci karen su ba bu babbaka kamar yadda mamallakin gidan nishadin, Sanusi Iliyasu Ishie ya bayyana.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da Mutane 7 a jihar Zamfara

'Yan bindiga sun yi garkuwa da Mutane 7 a jihar Zamfara
Source: UGC

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Zamfara, SP Muhammadu Shehu, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari da cewar tuni jami'an tsaro su bazama wajen gudanar da bincike da laluben miyagun ma'abota tayar da zaune tsaye.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, yayin da 'yan ta'addan suka fara yiwa masu kallon kwallon dauki dai-dai, ya sanya suka ankara cikin razani na neman tsira tare da yekuwa ta kawo ma su dauki.

KARANTA KUMA: 2019: Tambuwal ya gudanar da taron yakin neman zabe a bainar tsirarin al'umma

Hakan ya sanya da taimakon kawanya gami da tara-tara masu ta'adar suka samu nasarar cafke Mutane bakwai kuma suka yi awon gaba da su da kawowa yanzu ba bu amo ballantana labarin inda suka shiga.

Cikin wani rahoton mai nasaba da yiwa kasa fasadi, mun samu cewa an yi gamo da wata takardar katse kashi da kuma share-sharen najasa da ake cewa Toli Paper dauke da rubutun sunan Allah Khaliqu da a halin yanzu rahoton ke ci gaba da yaduwa a dandalan sada zumunta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel