2019: Tambuwal ya gudanar da taron yakin neman zabe a bainar tsirarin al'umma

2019: Tambuwal ya gudanar da taron yakin neman zabe a bainar tsirarin al'umma

- Al'umma sun kauracewa taron yakin neman zaben gwamna Tambuwal a garin Sabon Birni na jihar Sakkwato

- Gwamna Tambuwal ya samu tabarraki na yalwar al'umma yayin taron yakin neman zaben sa a garin Isa

- Tsohon gwamnan jihar Attahiru Bafarawa ya yi kira kan zaben gwamna Tambuwal a jihar Sakkwato

A yayin da kowane dan siyasa da irin salon kidan da ya karbe shi, mun samu cewa, al'umma sun kauracewa taron yakin neman zaben dan takarar kujerar gwamnan jihar Sakkwato na jam'iyyar PDP, Aminu Waziri Tambuwal.

Taron da aka gudanar a yau Lahadi cikin garin Sabon Birni da ke Gabashin jihar Sakkwato bai samun albarkar al'umma ba kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Maruwaita da ma su hasashe sun bayyana cewa, ‘yan tsirarin mutane sun halarci taron a karamar Sabon Birni da ta kasance babbar cibiyar magoya baya na jam'iyyar APC kuma mahaifa ga Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir na jam'iyyar APC.

2019: Tambuwal ya gudanar da yakin neman zabe a bainar tsirarin al'umma

2019: Tambuwal ya gudanar da yakin neman zabe a bainar tsirarin al'umma
Source: Twitter

Ko shakka ba bu al'ummar yankin sun tabbatar da akidar su ta goyon bayan jam'iyyar APC da hakan yayi tasiri wajen kauracewa taron yakin neman zabe na jam'iyyar adawa ta PDP.

Gabanin wannan taro, Gwamna Tambuwal ya gudanar da taron yakin neman zaben sa a garin Isa da ke karkashin karamar hukumar Isa inda ya samu yalwar al'umma magoya baya yayin da ya jaddada ma su daurin damarar sa ta inganta harkokin ilimi da kuma noma domin habaka tattalin arziki a fadin jihar.

KARANTA KUMA: Gabanin taron yakin neman zabe, Buhari ya gana da Sarakunan gargajiya na jihar Osun

Tambuwal ya kuma bayar da tabbacin sa ga al'ummar jihar wajen samar da ababen habaka tattalin arziki ta hanyar shimfida tsare-tsare na bayar da tallafin hannayen jari musamman ga Mata da kuma Matasa.

Cikin zayyana na sa jawaban, tsohon gwamnan Jihar Attahiru Bafarawa, ya bayyana farin cikin sa dangane da dumbin al'ummar da suka halarci taron yakin neman zabe da nuna goyon bayan, inda ya ce Gwamna Tambuwal shine mafificin zabe a gare su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel