2019: Jam’iyyar APGA reshen Zamfara ta tsayar da Buhari a matsayin dan takararta

2019: Jam’iyyar APGA reshen Zamfara ta tsayar da Buhari a matsayin dan takararta

- Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance reshen jihar Zamfara ta tsayar da Buhari a matsayin dan takararta a zaben watan gobe

- Dan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar APGA a jihar, Alhaji Abdullahi Sani, ya bayyana hakan a lokacin kamfen din jam’iyyar

- Sani yace sun gamsu da yaki da cin hanci da rashawar shugaban Buhari, da kuma yadda ya magance kalubalen tsaro, samar da ayyuka da kuma manufar noma

Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) reshen jihar Zamfara ta tsayar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Muhammadu Buhari a matsayin dan takararta a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu.

Dan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar APGA a jihar, Alhaji Abdullahi Sani, ya bayyana hakan a lokacin kamfen din jam’iyyar a Gusau a ranar Asabar.

2019: Jam’iyyar APGA reshen Zamfara ta tsayar da Buhari a matsayin dan takararta

2019: Jam’iyyar APGA reshen Zamfara ta tsayar da Buhari a matsayin dan takararta
Source: UGC

Sani ya bayyana cewa jam’iyyar ta gamsu da yaki da cin hanci da rashawar shugaban Buhari, da kuma yadda ya magance kalubalen tsaro, samar da ayyuka da kuma manufar noma.

Ya ce wadannan manufofin yayi daidai da APGA da shirin APGA na son sauya yanayin tattalin arzikin kasar.

KU KARANTA KUMA: Hanyoyi 5 da mutum zai bi don hana furfura fitowa a jikinsa

Dani ya kuma ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali sosai wajen habbaka fannin lafiya, da tsaro a jihar.

Ya sha alwashin gina cibiyoyin karbar haihuwa 147 a fadin kananan hukumom 14 na jihar da kuma cibiyoyin kula da masu yoyon fitsari uku, inda kowani yanki zai ja guda daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel