Dangane da korar Onnoghen: NJC za ta gudanar da muhimmin taro ranar Litinin

Dangane da korar Onnoghen: NJC za ta gudanar da muhimmin taro ranar Litinin

Majalisar shari'a ta kasa NJC ta kira wani muhimmin taron gaggawa domin tattaunawa akan korar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa mai shari'a Walter Onnoghen daga mukamin Alkalin Alkalai na kasa CJN.

Rahotanni sun bayyana cewa taron zai gudana ne a ranar Litinin, da misalin karfe 10 na safe, a babban birnin tarayya Abuja.

Majiya daban daban sun bayyana cewa, Onnoghen wanda aka dakatar da shi, ya zama kanun labarai da ke zagaya a kasar dama kasashen ketare, yayin da kuma rahotanni suka bayyana cewa ana sa ran mukaddashin Alkalin Alkalai na kasar, Ibrahim Muhammed ya jagoranci zaman taron.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Aisha Buhari ta karyata masu cewa ta yi Allah-wadai da korar Onnoghen

Dangane da korar Onnoghen: NJC za ta gudanar da muhimmin taro ranar Litinin

Dangane da korar Onnoghen: NJC za ta gudanar da muhimmin taro ranar Litinin
Source: UGC

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa, Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta karya rahotannin da ake yadawa na cewar ta yi Allah-wadai da hukuncin da shugaban kasa Buhari ya dauka na korar mai shari'a Walter Onnoghen daka mukamin Alkalin Alkalai na kasa (CJN).

Mrs Buhari a cikin wata sanarwa ta hannun Daraktanta na watsa labarai, Mr Suleiman Haruna da ya rabawa manema labarai a ranar Asabar a Abuja, ta bayyana wannan labarin da ake yadawa na cewa ta yi Allah-wadai da korar Onnoghen a matsayin 'labarin kanzon kurege'.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel