Aiki-ga-mai-kare-ka: Rundunar sojin Najeriya ta soma kera motocin yaki

Aiki-ga-mai-kare-ka: Rundunar sojin Najeriya ta soma kera motocin yaki

Rundunar sojin Najeriya a karkashin jagorancin Safsan ta, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai sun soma kera motocin sulke da na yaki manya da kanana domin fuskantar abokan gaba da sauran masu tada kayar baya a kamfanin su dake a jihar Kaduna.

Da yake bude kamfanin, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai a ranar Asabar din da ta gabata ya ce nan da shekara ta 2030, kamfanin zai soma kerawa sauran kasashen Afrika da ma duniya baki daya motocin.

Aiki-ga-mai-kare-ka: Rundunar sojin Najeriya ta soma kera motocin yaki

Aiki-ga-mai-kare-ka: Rundunar sojin Najeriya ta soma kera motocin yaki
Source: Facebook

KU KARANTA: Bariki: Wata tsaleliyar budurwa ta haukace bayan saurayin ta ya ajiye ta

Legit.ng Hausa ta samu cewa Buratai ya kuma da cewa yanzu da suka soma wannan kere-keren, za su samu isassun motocin da za su cigaba da tunkarar 'yan ta'addan Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

Buratai ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta kafa kamfanin ne na Nigerian Army Vehicle Manufacturing Company (NAVMC) a turance da nufin samar wa da jami'an tsaron kasar da motocin da suke bukata zuwa shekarar 2025 yayin da kuma zuwa 2030, a fara saidawa kasashen waje.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin manyan masana harkokin shari'a kuma mai sharhi akan lamurran yau da kullum, Farfesa Itse Sagay (SAN) ya bayyana matakin dakatarwa da shugaba Buhari ya dauka kan Alkalin-Alkalin Maishari'a Walter Onnoghen a matsayin wanda ya kamata kuma ya dace.

Farfesa Sagay ya bayyana cewa shugaba Buhari yayi abunda ya kamata a shari'ance domin ya yi biyayya ga umurnin kotun tabbatar da da'ar ma'aikata da ta bukaci ya dakatar da alkalin alkalan.

Ga dai kadan daga cikin hotunan motocin:

Aiki-ga-mai-kare-ka: Rundunar sojin Najeriya ta soma kera motocin yaki

Aiki-ga-mai-kare-ka: Rundunar sojin Najeriya ta soma kera motocin yaki
Source: Facebook

Aiki-ga-mai-kare-ka: Rundunar sojin Najeriya ta soma kera motocin yaki

Aiki-ga-mai-kare-ka: Rundunar sojin Najeriya ta soma kera motocin yaki
Source: Facebook

Aiki-ga-mai-kare-ka: Rundunar sojin Najeriya ta soma kera motocin yaki

Aiki-ga-mai-kare-ka: Rundunar sojin Najeriya ta soma kera motocin yaki
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel