ASUU na iya kawo karshen yajin aiki kwanan nan – Gwamnatin tarayya

ASUU na iya kawo karshen yajin aiki kwanan nan – Gwamnatin tarayya

- Ministan ilimi, Adamu Adamu, yace babu mamaki daliban jami’a a fadin kasar na iya komawa makarantunsu kwanan nan

- Sai dai kuma, ASUU sun ce lallai malaman jami’a ba za su dawo bakin aiki ba idan har gwamnatin tarayya ba ta cika masu bukatunsu ba

- Biodun Ogunyemi, shugaban kungiyar ASUU yace gwamnatin tarayya ta ki biyan naira biliyan 50 na kawo ci gaba da kungiyar ta nema daga gare ta

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daliban makarantun jami’a na iya komawa makarantun daban-daban kwanan nan yayinda kungiyar malaman jami’a (ASUU) na iya janye yajin aikinsu nan da mako guda fara daga ranar Litinin, 28 ga watan Janairu.

Ministan ilimi, Adamu Adamu, da yake jawabi ga yan jarida bayan wani taron manema labarai a ranar Juma’a, 25 ga watan Janairu yace akwai alamu na cewa malaman makarantun jami’a za su janye yajin aikinsu kwanan nan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

ASUU na iya kawo karshen yajin aiki kwanan nan – Gwamnatin tarayya

ASUU na iya kawo karshen yajin aiki kwanan nan – Gwamnatin tarayya
Source: UGC

“Watakila, zuwa mako mai zuwa, Ina kyautata zaton yajin aikin ASUU zai zo karshe,” inji ministan ilimi.

Sai dai kuma, ASUU sun ce lallai malaman jami’a ba za su dawo bakin aiki ba idan har gwamnatin tarayya ba ta cika masu bukatunsu ba.

Da yake Magana a ranar Laraba, 23 ga watan Janairu, Biodun Ogunyemi, shugaban ASUU, ya bayyana cewa naira biliyan 50 shine mafi kankantar abunda kungiyar ke nema daga gwanatin tarayya a farkon kwatan shekarar 2019 a matsayin kudin kawo ci gaba, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Sanatan APC ya maida martani ga shirin majalisar dokoki na daukar tsattsauran mataki kan Buhari saboda dakatar da Onnoghen

Ogunyemi ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa ba wai kin biyan kudin kawai gwamnatin tarayya tayi ba, bata nunaalamun cewa za ta saki kudin.

Da yake martani akan ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta saki naira biliyan 15.4 a matsayin wani bangare na biyan albashin malaman jami’a, yace: “Ba mu tabbatar ba a dai rana ta Laraba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel