Addini ba zai tasiri ba a zaben gwamnan jihar Kaduna - PDP

Addini ba zai tasiri ba a zaben gwamnan jihar Kaduna - PDP

- PDP ta ce addinin ba zai tasiri ba wajen karkatar da alkibilar nasara a yayin zaben gwamnan jihar Kaduna

- Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce al'ummar jihar Kaduna za su duba cancantar wajen zaben gwamna a zaben bana

- Ta ce hakan take yayin zaben kujerar shugaban kasa tsakanin Atiku da kuma Buhari

Da sandin shafin jaridar Vanguard mun samu cewa, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa, ba bu wani tasiri ko rawa da addini zai takaka wajen tabbatar da alkibilar sakamakon zaben gwamnan jihar Kaduna a zaben bana.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Kakakin cibiyar yakin neman zaben jam'iyyar PDP, Mista Ben Bako, shine ya yi furucin hakan yayin ganawa da mamena labarai a yau Lahadin cikin Jos na jihar Filato.

Gwamna El-Rufa'i tare da abokiyar takarar sa; Dakta Hadiza Balarabe

Gwamna El-Rufa'i tare da abokiyar takarar sa; Dakta Hadiza Balarabe
Source: Twitter

Bako ya ce al'ummar jihar Kaduna ba za ta yi la'akari da akidar addini ta gwamna Mallam Nasir El-Rufa'i ba, illa iyaka za ta yi duba zuwa ga kwazon sa bisa kujerar mulki domin tabbatar da cancantar sa wajen sake ba shi dama ta tsawon shekaru hudu ma su gabatowa.

Ya ce ko kadan akidar musulunci ta Gwamna El-Rufa'i da abokiyar takarar sa, Dakta Hadiza Balarabe, ba za tayi tasiri wajen samun nasarar sa a zaben watan jibi face nazari da duba ya zuwa kwazon sa tsawon shekaru da ya shafe a bisa kujerar mulki.

Kakakin jam'iyyar ya ce, a bana addini ba zai tasiri ba wajen zaben gwamnan jihar Kaduna sakamakon tarayyar akida ta musulunci ga dukkanin manyan 'yan takara biyu na jam'iyyar APC da kuma PDP, Isa Ashiru.

KARANTA KUMA: Rashin doka da tsari ya sanya ake fataucin Matan Najeriya zuwa kasar Saudiyya

Baya ga jihar Kaduna, Bako ya ce akidar addini ba za ta yi tasiri ba wajen tabbatar da cancantar dan takara a zaben kujerar shugaban kasar Najeriya tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na PDP.

Ya kara da cewa, a halin yanzu al'ummar Najeriya sun hada kawunan su wuri guda domin zaben dan takara mafi cancantar jagoranci ba tare da la'akari da addinin sa ba ko kuma tasiri na jam'iyyar sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel