Allura-ta-tono-galma: Sabon bincike ya bankado wasu sirrikan Alkalin-alkalai Onnoghen

Allura-ta-tono-galma: Sabon bincike ya bankado wasu sirrikan Alkalin-alkalai Onnoghen

Wani sabon bincike da mahukunta a Najeriya suka gudanar akan Alkalin-Alkalai, Mai shari'a Walter Onnoghen da shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar ya gano asusun bankuna akalla hudu da yake da su kuma dukkanin su shake da kudaden Najeriya da kuma kasar waje.

Mun samu cewa mahukuntan da aka dorawa alhakin yin binciken dai sun aikawa bankuna akalla uku takarda suna bukatar sanin ainihin kudaden da ke a cikin asusun Alkalin Alkalan da yanzu haka ke cigaba da fuskantar kalubale da dama.

Allura-ta-tono-galma: Sabon bincike ya bankado wasu sirrikan Alkalin-alkalai Onnoghen

Allura-ta-tono-galma: Sabon bincike ya bankado wasu sirrikan Alkalin-alkalai Onnoghen
Source: UGC

KU KARANTA: An gano sabuwar hanyar magudi da Atiku ya shirya

Legit.ng Hausa ta samu cewa bankunan da aka tuntuba game da shi Mai Shari'a Walter Onnoghen din sun hada ne da bankin Standard Chartered Bank, bankin Union Bank da kuma Heritage Bank kuma dukkanin su su bayar da hadin kai.

Binciken dai ya tabbatar da cewa Alkalin Alkalan yana da dumbin kudaden da suka fi karfin samun halaliyar sa kuma yanzu haka ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Ga dai cikakken bayanan abun da aka samu a cikin asusun nashi nan:

1. Asusun dalar Amurka — $1,922,657.00

2. Asusun kudin Ingila na Faund — £138, 439.00

3. Asusun kudin tarayyar nahiyar Turai na Yuwro — €55,154.00

4. Asusun kudaden Naira — N91, 962.362.49

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel