Jami’an tsaro sun haramtawa ‘Yan jarida ganawa da Walter Onnoghen

Jami’an tsaro sun haramtawa ‘Yan jarida ganawa da Walter Onnoghen

Mun samu labari cewa ‘yan jarida sun gaza shiga cikin gidan Walter Onnoghen wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da kujerar sa ta Alkalin Alkalan Najeriya a Ranar Juma’ar nan.

Jami’an tsaro su haramtawa ‘Yan jarida ganawa da Walter Onnoghen

An hana ‘Yan jarida ganin Onnoghen a gidan sa da ke kusa da Kotun koli
Source: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa Jami’an tsaro sun ki bari manema labarai su iya shiga cikin gidan babban Alkali mai shari’a Onnoghen wanda shugaban kasa Buhari ya dakatar da mukamin sa domin zantawa da shi ko ganewa idanun su..

Wani ma’aikacin jarida da yayi kokarin shiga cikin gidan ya gamu da cikas daga wajen Jami’an tsaro masu fararen kaya watau DSS da kuma wasu ‘yan sanda wanda su kace babu wanda ya isa ya ziyarci Onnoghen din a wannan lokaci.

KU KARANTA: Babu ruwa na: Aisha Buhari ta karyata cewa ta yi magana kan dakatar da Onnoghen

Kamar yadda mu ka ji, wadannan jami’an tsaro su na dauke ne da tambarin fadar shugaban kasa, kuma sun murtuke fuska sun hana a iya haduwa da Alkalin Alkalan da aka dakatar daga mukamin sa saboda zargin rashin gaskiya.

Jami’an na DSS sun fadawa ‘yan jarida cewa ba za su iya shiga gidan Mai shari’a Walter Onnoghen ba har sai idan sun samu goron gayyata. Ko da su ka ga babu wanda ya gayyace su, sai su ka tasa keyar ‘yan jaridan zuwa wajen gida.

Kasashen waje sun yi tir da dakatar da Onnoghen daga kujerar CJN da aka yi. Sai dai Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta bari wasu kasashen ketare su rika shiga cikin sha’anin da bai shafe su ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel