Sanatan APC ya maida martani ga shirin majalisar dokoki na daukar tsattsauran mataki kan Buhari saboda dakatar da Onnoghen

Sanatan APC ya maida martani ga shirin majalisar dokoki na daukar tsattsauran mataki kan Buhari saboda dakatar da Onnoghen

- Sanata Ali Ndume yace makirci don tsige shugaba Buhari ba zai yi tasiri ba

- Dan majalisan na APC yace shugaban kasar bai take kowani doka ba don ya dakatar da Onnoghen

- Majalisar dokokin kasar na shirin dawwa daga hutu biyo bayan matakin da shugaban kasar ya dauka

Sanata Ali Ndume yace yan majalisa a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba za su lamunci duk wani yunkuri na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari akan dakatar da Walter Onnoghen ba.

Tsohon shugaban majalisar yayi Magana a ranar Asabar, 26 ga watan Janairu cewa shugaban kasar bai take doka ba.

Sanatan APC ya maida martani ga shirin majalisar dokoki na daukar tsattsauran mataki kan Buhari saboda dakatar da Onnoghen

Sanatan APC ya maida martani ga shirin majalisar dokoki na daukar tsattsauran mataki kan Buhari saboda dakatar da Onnoghen
Source: Depositphotos

Yace: “A matsayin mambobin jam’iyyar APC a majalisar dokoki, za mu sanya ra’ayin kasa sama da kowace akida ko duba bangare wajen magance lamura.

“Don haka, duk wanda ke son fara wani rigima a majalisar dokoki kan lamarin, mun shirya masa. Muna da yawan adadin da karfi saboda mune masu rinjaye.

KU KARANTA KUMA: Jirgin farko ya sauka a sabon tashar jirgin ruwa na Baro

“Kawai dai shugabancin majalisar dattawan na son tashin-tashina ne, idan ba haka ba, shugabancin da ya zargi bangaren shari’a da kuts a cikin lamuranta yanzu kuma sai gashi yana adawa da shugaban kasa akan yaki da rashawa a wannan bangare na gwamnati.”

Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 25 ga watan Janairu 2019 ya dakatar da alkalin-alkalan Najeriya Walter Onnoghen sannan ya nada Ibrahim Tanko Muhammed daga jihar Bauchi a matsayin mukaddashin shugaban alkalan kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel