Gwamna Ganduje ya ki halartar muhawarar zabe a Jihar Kano

Gwamna Ganduje ya ki halartar muhawarar zabe a Jihar Kano

- Jiya ne aka yi muhawara tsakanin masu neman kujerar Gwamnan Kano

- Gwamna Ganduje wanda ke kan gadon mulki bai halarci muhawarar ba

Gwamna Ganduje ya ki halartar muhawarar zabe a Jihar Kano

Abdullahi Ganduje ya ki halartar muhawarar takarar Gwamnan Kano
Source: Facebook

Mun samu labari cewa a cikin karshen makon nan ne aka shirya muhawara tsakanin masu takarar kujerar gwamnan jihar Kano a zaben da za ayi cikin ‘yan kwanaki kadan masu zuwa. Sai dai gwamna mai-ci bai halarci zaman ba.

Kamar yadda mu ka ji, ‘dan takarar PDP Abba Kabiru Yusuf da Salihu Sagir Takai na jam’iyyar PRP wanda su ne manyan masu harin kujerar gwamnan na Kano sun yi muhawarar. Gwamna Ganduje kuwa gaba daya bai iya zuwa wajen ba.

Nasiru Yusuf na jam’iyyar Labor Party yana cikin wadanda aka tafka muhawarar da shi inda ya bayyana shirin da yake da shi na mulkar jihar Kano idan har ya samu nasara a zabe. Za ayi zaben ne a farkon watan Maris na shekarar bana.

KU KARANTA: Buhari ya sayar da tashar jirgin Gwamnati ga 'Yan kasuwa

Injiniya Abba Yusufu ya bayyana cewa zai karasa manyan ayyukan da gwamnatin Rabiu Kwankwaso ya fara wadanda su ka hada da tituna a kowace karamar hukuma. Abba Yusuf ya kuma yi alkawarin inganta harkar lafiya.

‘Dan takarar na PDP dai ya tabbatar da cewa yana da wasu kudirori 11 da ya sa gaba idan ya samu mulki. An shirya wannan muhawara ne a wani sashe na bincike da kuma cibiyar nazari na Aminu Kano domin ‘yan takarar su fito da kan su.

BBC Hausa dai za ta gudanar da na ta muhawarar a ranar 31 ga watan Janairun nan da safe. Ana sa rai Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Abba Kabir Yusuf, da Salihu Sagir Takai da Mustapha Getso da Maimuna Mohammed za su halarta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel