Buhari ya sayar da tashar jirgin Gwamnati ga 'Yan kasuwa akan N105bn

Buhari ya sayar da tashar jirgin Gwamnati ga 'Yan kasuwa akan N105bn

Mun samu cewa, a yayin neman rangwantawa kanta nauyi, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta sayar da wata babbar kadarar ta ga 'yan kasuwa domin su ci gaba da daukar nauyin fadi-tashin ta.

Ma'aikatar kula da saye da sayarwar kadarorin gwamnatin tarayya, ta rattaba hannu kan yarjejeniyar sayar da wata tsohuwar tashar jirgin ruwa ta Warri dake jihar Delta ga kamfanin Ocean and Cargo Terminal Services Limited.

Cikin sanarwar da sa hannun Alex Okoh, shugaban ma'aikatar a ranar Talata ta makon da ya gabata ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta sayarwa da kamfanin Ocean and Cargo Terminal Services Limited tsohuwar tashar Warri akan dalar Amurka miliyan 100.78 da ya yi daidai da Naira biliyan 105 a kudin kasar nan.

Buhari ya sayar da tashar jirgin Gwamnati ga 'Yan kasuwa akan N105bn

Buhari ya sayar da tashar jirgin Gwamnati ga 'Yan kasuwa akan N105bn
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kamfanin Ocean and Cargo Terminal Services Limited, ya samu nasarar sayen wannan tasha yayin da ya sanya farashi mafi daraja fiye da sauran 'yan kasuwanni da su ka nemi mallakar ta.

Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar sayar da babbar tashar ga 'yan kasuwa yayin wata ganawa ta da ta gudanar tun a ranar 12 ga watan Yunin shekarar da ta gabata. Cikin 'yan kasuwanni bakwai da suka nemi mallakin ta bayan tantance cancantar su daya daga ciki ya zamto zakara.

KARANTA KUMA: Najeriya ta na karkashin kyakkyawar kulawa a hannun Miji na - Aisha Buhari

Mista Okoh ya ce babbar manufar sayar da wannan kadara ba ta wuce neman inganta harkokin gudanarwar ta ba musamman ta bangaren jigilar haja cikin sauki gami da saukaka nauyin fadi-tashin ta a wuyan gwamnatin tarayya.

A sanadiyar haka gwamnatin tarayya ta gargadi kamfanin na Ocean and Cargo Terminal Services Limited, da ya yi riko da duk wasu tsare-tsare gami da tabbatar da da'a kan yarjejeniyar da ya kulla yayin sayen tashar a hannun ta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel