Babbar magana: Aisha Buhari ta karyata masu cewa ta yi Allah-wadai da korar Onnoghen

Babbar magana: Aisha Buhari ta karyata masu cewa ta yi Allah-wadai da korar Onnoghen

- Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta karya rahotannin da ake yadawa na cewar ta yi Allah-wadai da hukuncin Buhari ya yanke na korar mai shari'a Walter Onnoghen

- Mrs Buhari ta bayyana wannan labarin da ake yadawa na cewa ta yi Allah-wadai da korar Onnoghen a matsayin 'labarin kanzon kurege'

- Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa shugaba Buhari ya kori tsohon CJN, Walter Onnoghen bayan samun umurnin hakan daga kotun da'ar ma'aikata (CCT)

Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta karya rahotannin da ake yadawa na cewar ta yi Allah-wadai da hukuncin da shugaban kasa Buhari ya dauka na korar mai shari'a Walter Onnoghen daka mukamin Alkalin Alkalai na kasa (CJN).

Mrs Buhari a cikin wata sanarwa ta hannun Daraktanta na watsa labarai, Mr Suleiman Haruna da ya rabawa manema labarai a ranar Asabar a Abuja, ta bayyana wannan labarin da ake yadawa na cewa ta yi Allah-wadai da korar Onnoghen a matsayin 'labarin kanzon kurege'.

"An ankarar da uwar gidan shugaban kasa kan wani labari da ake yadawa a kafofin sada zumunta na zamani wanda har ake cewa ta yi Allah-wadai da dakatarwar da aka yiwa Walter Onnoghen, daga mukamin Alkalin Alkalai na kasa."

KARANTA WANNAN: Da duminsa: NBA za ta yi taron gaggawa tare da yin zanga zanga kan korar Onnoghen

Babbar magana: Aisha Buhari ta karyata masu cewa ta yi Allah-wadai da korar Onnoghen

Babbar magana: Aisha Buhari ta karyata masu cewa ta yi Allah-wadai da korar Onnoghen
Source: Depositphotos

Sanarwar ta ce: "Yana da kyau 'yan Nigeria su sani cewa uwar gidan shugaban kasa bata fitar da wata sanarwa kan hakan ba, wannan zai tabbatar da cewa labarin da ake yadawa karya ce tsagwaronta.

"Kuma labarin da ake yadawa kan hakan abun Allah-wadai ne, haka zalika muna kira ga masu yada irin wannan jita-jitar da su kauracewa yin hakan daga yanzu ko su fuskanci fushin shari'a idan suka shiga hannu," a cewar sanarwar.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori tsohon CJN, Walter Onnoghen bayan samun umurnin hakan daga kotun da'ar ma'aikata (CCT).

Wannan korar kamar yadda kotun CCT ta bayyana, zai taimaka mata wajen sauraron karar da aka shigar akan Onnoghen, bisa zarginsa da kin bayyana wasu makudan kudade da ya mallaka a wani asusun banki kamar yadda kundin dokar NAN ta bukata.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel