Da duminsa: NBA za ta yi taron gaggawa tare da yin zanga zanga kan korar Onnoghen

Da duminsa: NBA za ta yi taron gaggawa tare da yin zanga zanga kan korar Onnoghen

- Kungiyar lauyoyi (NBA) a ranar Litinin zata gudanar da taron gaggawa na kwamitin mahukuntan kungiyar na kasa (NEC) akan korar Walter Onnoghen

- Kiran wannan taron na gaggawa zai tilasta rufe kotuna da kuma tilasta fitowar kowanne lauya har sai an kammala taron da kuma zanga zangar

- NBA zata gabatar da bukata ga shugaban kasa Buhari na ya daina yiwa fannin shari'ar rikon sakainar kashi tare da soke dakatarwar da ya yiwa mai shari'a Walter Onnoghen

Kungiyar lauyoyi (NBA) a ranar Litinin zata gudanar da taron gaggawa na kwamitin mahukuntan kungiyar na kasa (NEC) akan hukuncin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke na korar mai shari'a Walter Onnoghen daga mukamin Alkalin Alkalai na kasa (CJN).

Shugaban kasar, a ranar Juma'a ya sanar da dakatar da Onnoghen, wanda ke fuskantar tuhuma a kotun da'ar ma'aikata (CCT) kan zargin da ake masa na kin bayyana wasu makudan kudaden kasashen waje da ya mallaka a wasu asusun banki, inda kuma a nan take shugaban kasar ya nada mai shari'a Ibrahim Tanko a matsayin mukaddashin Alkalin Alkalan.

Babban sakataren kungiyar NBA, Jonathan Gunu Taidi, ya sanar da kiran taron da zanga zangar a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, cewar sun shirya gudanar da taron ne domin tattaunawa kan dakatarwar da aka yi Onnoghen, kuma mambobin NEC na kungiyar ne kadai zasu halarta.

KARANTA WANNAN: Mu leka kotu: Wata mahaifiya ta bukaci a maidawa diyarta 'yar shekaru 4 budurcinta

Da duminsa: NBA za ta yi taron gaggawa tare da yin zanga zanga kan korar Onnoghen

Da duminsa: NBA za ta yi taron gaggawa tare da yin zanga zanga kan korar Onnoghen
Source: UGC

Kiran wannan taron na gaggawa da kungiyar NBA ta yi, wanda zata gudanar a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu, 2019, zai tilasta rufe kotuna da kuma tilasta fitowar kowanne lauya har sai an kammala taron da kuma zanga zangar.

Jaridar Tribune Online ta tattara rahoto kan cewar bayan kammala taron, kungiyar ta shirya gudanar da zanga zangar lumana akan wannan cin fuska da ake yiwa fannin shari'a, wanda za su gudanar a shelkwatar kungiyar NBA da ke Abuja.

Za a fara zanga zangar ne daga shelkwatar NBA inda ake sa ran 'yan Nigeria za su bukaci abu daya daga wajen shuwagabannin lauyoyin Nigeria, shine nuna karfin ikon snhugabancin ta hanyar tilasta fitowar lauyoyi daga kotuna da kuma ci gaba da matsin lamba har sai shugaban kasa ya daina yiwa fannin shari'ar rikon sakainar kashi tare da soke dakatarwar da ya yiwa mai shari'a Walter Onnoghen.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel