Najeriya ta na karkashin kyakkyawar kulawa a hannun Miji na - Aisha Buhari

Najeriya ta na karkashin kyakkyawar kulawa a hannun Miji na - Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, ta yi karin haske da tsokaci na jan hankalin al'ummar Najeriya dangane da halin da kasar nan za ta ci gaba da kasancewa muddin aka sake zaben mijin ta a zaben watan gobe.

Mun samu cewa, uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, ta yi kira ga Mata da kuma Matasan jihar Kogi da su jefa kuri'un su ga mai gidan ta, Muhammadu Buhari a yayin babban zaben kasa domin ci gaba da samun kyakkyawar kulawa a karkashin jagorancin sa.

Najeriya ta na karkashin kyakkyawar kulawa a hannun Miji na - Aisha Buhari

Najeriya ta na karkashin kyakkyawar kulawa a hannun Miji na - Aisha Buhari
Source: UGC

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Hajiya Aisha ta yi kira gami da gargadin na neman al'ummar jihar Kogi da su fito kwansu da kwarkwata wajen goyon bayan kudirin tazarcen shugaban kasa Buhari domin ci gaba da samun kyakkyawar kulawa ta jagorancin sa.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana hakan ne yayin wani zama na sauraron ra'ayin al'umma na Mata da kuma Matasa da kungiyar yakin neman zaben Buhari ta dauki nauyin gudanarwa a babban birnin Lokoja.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, mai fada a ji kuma jagorar Mata ta kungiyar yakin neman zaben Buhari, Hajiya Salamatu Umar-Eluma, ita ta ce ta yi ruwa da tsaki wajen daukar nauyin wannan babban taro a tantagwaryar jihar Kogi.

KARANTA KUMA: 2019: Buhari zai sha mamakin nasarar Atiku a yankin Kudu maso Yamma - PDP

Ko shakka ba bu, Aisha Buhari ta yi wannan kira gami da gargadi da sanadin Misis Dolapo Osinbajo, uwargidan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da ta wakilce ta yayi babban taron.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsagerun Neja Delta sun yiwa shugaba Buhari jinjina bisa matakin da ya dauka na dakatar da alkalin alkalai na Najeriya, Mai shari'a Walter Onnoghen.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel