Babbar magana: Amurka, Birtaniya da EU sun yi tsokaci kan dakatar da Onnoghen

Babbar magana: Amurka, Birtaniya da EU sun yi tsokaci kan dakatar da Onnoghen

- Tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Alkalin Alkalai na kasa, mai shari'a Walter Onnoghnen, 'yan Nigeria suka fara tofa albarkacin bakinsu

- Kungiyar Tarayyar Turai, Amurka da Birtaniya sun fito fili tare da bayyana takaicinsu da kuma damuwa karara akan wannan mataki na dakatar da mai shari'a Onnoghen

- Burtaniya a hannu daya kuwa ta ce wannan matakin da Buhari ya dauka zai iya kawo babban sabani ko haddasa rikicin siyasa a zaben kasar mai zuwa

Tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Alkalin Alkalai na kasa, mai shari'a Walter Onnoghnen, 'yan Nigeria suka fara tofa albarkacin bakinsu musamman ma a kafafen sada zumunta na yanar gizo. Sai dai, ba a iya 'yan Nigeria kadai lamarin ya tsaya ba, hatta kasashen duniya sunyi caa kan Nigeria, dangane da wannan matakin shugaban kasar ya yanke.

Kungiyar Tarayyar Turai, Amurka da Birtaniya sun fito fili tare da bayyana takaicinsu da kuma damuwa karara akan wannan mataki na dakatar da mai shari'a Onnoghen, wanda aka shigar da shi kara kotun da'ar ma'aikata akan zarginsa da kin bayyana wasu makudan kudaden kasar waje da ya mallaka a asusunsa, kamar yadda dokar kotun ta tanadar.

Sai dai a hannu daya, kungiyar tarayyar Turai (EU) ta bukaci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma 'yan adawa, da su bi tsarin da doka ta tanadar, wajen warware wannan takaddama da kuma yin nazarin wannan mataki da shugaban kasa Buhari ya dauka da ya haifar da dakatar da Alkalin Alkalan.

KARANTA WANNAN: Jihar Kwara: Buhari da APC na kulla makircin cafke shuwagabanninmu - PDP

Babbar magana: Amurka, Birtaniya da EU sun yi tsokaci kan dakatar da Onnoghen

Babbar magana: Amurka, Birtaniya da EU sun yi tsokaci kan dakatar da Onnoghen
Source: UGC

Ita kuwa kasar Amurka, cewa ta yi an sauya alkalin alkan ba tare da shugaban kasa Buhari ya samun amincewar hadin gwiwar bangaren majaliosar dokokin kasar ba, wanda kuma hakan abun damuwane matuka.

Burtaniya a hannu daya kuwa ta ce wannan matakin da Buhari ya dauka zai iya kawo babban sabani ko haddasa rikicin siyasa a zaben kasar mai zuwa, kasancewar matakin zai iya shafar sahihancin zaben. A cewar kasar, bai kamata gwamnatin tarayya ta yanke wannan hukunci a gabar zaben ba.

Tuni dai dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya Atiku Abubakar, ya dakatar da yakin neman zabensa tsawon kwanaki uku, domin nuna adawa da matakin dakatar da mai shari’a Onnoghen daga mukaminsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.n

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel