2019: Buhari zai sha mamakin nasarar Atiku a yankin Kudu maso Yamma - PDP

2019: Buhari zai sha mamakin nasarar Atiku a yankin Kudu maso Yamma - PDP

A yayin da a halin yanzu kwanaki kalilan su ka rage a gudanar da babban zabe na kujerar shugaban kasa, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta yi bugun gaba na samun babban kaso na nasarar zaben a wani yanki na Najeriya.

Mun samu cewa, jam'iyyar adawa ta PDP ta ce nasarar dan takarar ta na kujerar shugaban kasa, Atiku Abubakar, za ta bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari mamakin gaske yayin babban zaben da za gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu na gobe.

Mataimakin babban sakataren jam'iyyar na kasa mai hulda da al'umma, Mista Diran Odeyemi, shine ya bayyana hakan da cewar akwai yaudara mai girman gaske ga wadanda su ka yiwa shugaba Buhari alkawalin samun nasara a yankin Kudu maso Yammacin kasar nan.

2019: Buhari zai sha mamakin nasarar Atiku a yankin Kudu maso Yamma - PDP

2019: Buhari zai sha mamakin nasarar Atiku a yankin Kudu maso Yamma - PDP
Source: UGC

Yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar The Punch cikin birnin Legas a ranar Juma'ar da ta gabata, kakakin jam'iyyar cikin bugun gaba ya bayyana cewa, Atiku zai lallasa Buhari a yankin Kudu maso Yamma da kuma sauran yankuna Najeriya.

Majiyar jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Mista Odeyemi ya yi martani dangane da ikirarin gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi da a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cewa, shugaba Buhari zai yi nasara a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.

Ajimobi ya bayyana cewa, duba da kwazon shugaba Buhari gami kasancewar mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo dan asalin yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, ya sanya nasarar sa ba za ta yi gamo da wani cikas ko tangarda ba.

KARANTA KUMA: Sai na dawowa da Najeriya dukkanin martabar ta - Atiku

Da ya ke ci gaba da raddi gami da martani, Mista Odeyemi ya ce ba bu abun zo a gani kuma na yabawa da shugaba Buhari ya yiwa yankin Kudu maso Yammacin kasar nan. Ya ce irin juya baya ya sanya al'ummar yankin za su ramawa Kura aniyarta yayin jefa kuri'u zaben watan gobe.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari, ta yi kira ga Matasa da kuma Mata akan goyon bayan shugaba Buhari domin kasar Najeriya ta ci gaba da samun kyakkyawar kulawa maras yankewa a karkashin jagorancin sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel