Jihar Kwara: Buhari da APC na kulla makircin cafke shuwagabanninmu - PDP

Jihar Kwara: Buhari da APC na kulla makircin cafke shuwagabanninmu - PDP

- Jam'iyyar PDP a jihar Kwara ta tada jijiyoyin wuya kan wani zargi da take yi na cewar jam'iyyar APC na kitsa tuggun kullawa wasu daga cikin mambobinta

- Shugaban PDP na jihar, Alhaji Kola Shittu ya lissafa wasu shuwagabannin jam'iyyar guda 7 da suke zargin APC ta kulla masu tuggun don a cafke su, kafin zuwan Buhari jihar

- A ranar 4 ga watan Fabreru, 2019 ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da yakin zaben sa jihar Ilorin, babban birnin jihar Kwara

Jam'iyyar PDP a jihar Kwara ta tada jijiyoyin wuya kan wani zargi da take yi na cewar jam'iyyar APC na kitsa tuggun kullawa wasu daga cikin mambobinta sharri kafin ziyarar kaddamar da yakin zabe da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar a ranar 4 ga watan Fabreru, 2019 a Ilorin.

Da yake jawabi ga manema labarai a Ilorin a ranar Asabar, shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Alhaji Kola Shittu wanda ya yi wannan zargin, ya lissafa wasu shuwagabannin jam'iyyar guda 7 da suke zargin APC da shugaban kasa sun shirya kulla masu tuggun don a cafke su, da nufin kawo rudani a cikin jam'iyyar.

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar sai ya bukaci 'yan Nigeria da su matsa lamba ga jami'an tsaro akan bukatar da ke akwai na kar su bari a yi amfani da su a matsayin karnukan farauta, yana mai cewa jam'iyyar ta kasance tana kaddamar da yakin zabenta a fadin jihar ba tare da ta taba cin karo da wata matsala ko karya doka ba.

KARANTA WANNAN: Cikakken bayani kan N27,000 da N30,000 na karin albashi - Ministan kwadago

Jihar Kwara: Buhari da APC na kulla makircin cafke shuwagabanninmu - PDP

Jihar Kwara: Buhari da APC na kulla makircin cafke shuwagabanninmu - PDP
Source: UGC

Ya ce: "Kamar yadda kuka sani shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya kai ziyara jihar Kwara a ranar 4 ga watan Fabreru, 2019 domin kaddamar da yakin zabensa. Muna maraba da shi a yayin da ya shigo jiharmu mai albarka.

"Sai dai, muna so mu jawo hankulan jama'a a kan wani yunkuri da jam'iyyar adawa ta APC ke yi a hjihar na gogawa wasu shuwagabannin jam'iyyarmu kashin kaji, da nufin cafke su kafin zuwan shugaban kasar jihar tamu.

"Rahotanni sun zo mana kan cewa an umurci jami'an tsaro da su cafke wadannan shuwagabannin jam'iyyar namu kafin zuwan shugaban kasar, bisa wasu dalilai na su na karya wanda APC ta shirya.

"Daga cikin manyan shuwagabannin jam'iyyarmu da aka shirya cafkewa ba bisa ka'ida ba akwai shuwagabannin shiyyar Arewa da ta tsakiya, Alhaji Isiaka Oniwa da Alhaji Jimoh Adesina. Sauran sun hada da Alhaji Musa Abdullahi, Mr Taju Alabi, Alhaji Oba Ajara, Alhaji Alfa Dembo, Barr. Lanre Daibu, Hon. Isiaka Magaji, Alhaja Sarat Adebayo, da dai sauransu.

"Muna son daukacin 'yan Nigeria da ma duniya su sani cewa babu wani mambanmu da ya aikata laifin da ya cancanci a cakfe shi gabanin zuwan shugaban kasa Buhari. Shuwagabanni da mambobin jam'iyyarmu sun kasance masu bin doka da oda, kuma masu son zaman lafiya da sauran jam'iyyun adawa," a cewar sa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel