Obasanjo na goyon bayan Atiku ne saboda tsoron abunda Buhari zai yi masa – Balarabe Musa

Obasanjo na goyon bayan Atiku ne saboda tsoron abunda Buhari zai yi masa – Balarabe Musa

- Alhaji Balarabe Musa ya bayyana cewa kasar nan bata da ka’idar zabe na gaskiy da amana

- Tsohon gwamnan yace daga APC har PDP suna kulla yadda za su yi magdin zabe ne

- Musa yace Obasanjo na goyon bayan Atiku ne saboda tsoron abunda Buhari zai yi masa

Alhaji Balarabe Musa ya bayyana cewa kasar nan bata da ka’idar zabe na gaskiy da amana sannan cewa kudi ne kadai zai tantance wanda zai yi nasara a zaben 2019.

A wata hira da jaridar Nigerian Tribune, tsohon gwamnan na tsohuwar jihar Kaduna ya kuma bayyana cewa goyon bayan da Cif Olusegun Obasanjo ke ba Atiku yana bashi ne don saboda yana tsoron abunda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi masa.

Musa yace koda dai za a yi yunkuri don gudanar da zabe na gaskiya da amana, duk da haka jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki da babbar jam’iyyar adawa Peoples Democratic Party (PDP) za su yi magudi.

Obasanjo na goyon bayan Atiku ne saboda tsoron abunda Buhari zai yi masa – Balarabe Musa

Obasanjo na goyon bayan Atiku ne saboda tsoron abunda Buhari zai yi masa – Balarabe Musa
Source: Depositphotos

Yace: “Komai na iya faruwa a Najeriya, amma abu guda shine kada mutane su bari a shashantar dasu cewa za a yi zabe na gaskiya da amana sannan a samu halattaciyar gwamnati da za ta yi jagoranci. Wadannan ka’idoji babu su. Don haka, za a yi yunkuri, tabbass, amma ba za a yi zabe na gaskiya ba da zai kai ga halattaciyar gwmnati ba. Za a yi magudin zabe don alfarma ga wadanda ked a kudi, saboda siyasar Najeriya a yanzu ta kudi ce. Musamman kudaden sata.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dalilin da yasa Buhari yayi gaggawan sallamar shugaban Alkalin Najeriya - Sabon bincike

“Ba za ka taba iya lashe zaben gwamna ba a Najeriya sai ka kashe akalla rabin naira biliyan. A kan zaben shugaban ksa kuwa, za ka kashe ko nawa ne fara daga naira biliyan 3 zuwa Naira biliyan 5. Yadda zaaben shugaban kasa na 2019 yke m yan takarar jam’iyyun All Progressive Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) za su kashe kusan naira biliyan 500 domin su yi nasarar hayewa kujerar shugaban kasa. Babu shakka za su siy kuti’u sannan za su siyi wadanda za su gudanar da kamfen din."

Musa ya kuma zargi Obasanjo da yi Kaman wan hukuma a mulkin mallaka cewa goyon bayan Atiku da yake yi saboda tsoron Buhari da yake ji ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel