Atiku: Gwamna Willie Obiano yayi kaca-kaca da Kungiyar Ohanaeze

Atiku: Gwamna Willie Obiano yayi kaca-kaca da Kungiyar Ohanaeze

Gwamnan jihar Anambra Mista Willie Obiano yayi kaca-kaca da shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo na Najeriya, Nnia Nwodo a ranar Alhamis din da ta gabata kamar yadda mu ka samu labari daga The Nation.

Atiku: Gwamna Willie Obiano yayi kaca-kaca da Kungiyar Ohanaeze

Gwamnan Ibo ya barranta daga mubaya'ar da aka yi wa Atiku
Source: Depositphotos

The Nation ta rahoto cewa Willie Obiano yayi tir da mubaya’ar da kungiyar Inyamuran tayi wa jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa. Gwamna yace wannan danyen aiki da kungiyar Ohanaeze tayi na kira a zabi Atiku a 2019 sakarci ne.

Kwanan nan ne Dr. Nnia Nwodo ya fitar da jawabi yana mai cewa kungiyar su ta Ohanaeze Ndigbo, za ta goyi bayan jam’iyyar PDP ne a zaben bana. Wannan abu bai yi wa Willie Obiano dadi ba inda har ta kai ya zagi Nnia Nwodo.

Mai girma Obiano yace kungiyar ta Ibo ta fito tana goyon bayan PDP a daidai lokacin da shugaba Buhari ya kaddamar da wani katafaren aiki na gwamnatin tarayya da sunan Marigayi Nnamdi Azikiwe a garin Onitsha bai dace ba.

KU KARANTA: Na yafewa Jam'iyyar mu ta APC - inji Gwamna Yari na Zamfara

Willie Obiano ya kira wannan aiki na kungiyar da sakarcin banza inda shi kuma Dr. Nnia Nwodo wanda shi ne shugaban kungiyar ta Ohanaeze Ndigbo ya nuna takaicin sukar da gwamnan yayi wa kungiyar har ya maida masa martani.

A sakon waya, shugaban na Ohanaeze Ndigbo, Nwodo, ya kira gwamnan na Anambra da sunayen da ba su dace ba a dalilin sukar sa da yayi. Dattijon yayi kaca-kaca da gwamnan yana mai masa gorin irin abubuwan da yayi masa a da.

KU KARANTA: Zaben 2019: Atiku ne zabin mu ba kowa ba – Inji kungiyar Ohanaeze

Nnia Nwodo ya fadawa gwamna Obiano cewa yana cikin wadanda su kayi kira ga kungiyar IPOB ka da tayi watsi da zaben Anambra, sannan kuma yace shi ne ya ba shugaban kasa hakuri aka dawo masa da jami’an tsaron da ke gadin sa.

Dattijon yace a wancan lokaci dai gwamnan bai kira sa Sakarai ba, sai don kurum ya nemi jama’a su zabi Atiku a wannan karo. Dr. Nwodo yace wata rana nan gaba za a gane wanane Sakarai tsakanin shi da gwamna na jihar Anambra.

Gwamna Obiano dai bai yi na’am da goyon bayan da kungiyar Ohanaeze ta ba Atiku Abubakar na PDP a zaben bana ba. Gwamnan duk da yana jam’iyyar adawa ta APGA ba ya tare da Atiku a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel