Ba za mu bari wata kasa ta rika yi mana katsalandan ba – Najeriya ta fadawa Amurka

Ba za mu bari wata kasa ta rika yi mana katsalandan ba – Najeriya ta fadawa Amurka

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta bari wasu kasashen waje su rika shiga cikin sha’anin da bai shafe su game da harkar Najeriya ba. A jiya ne shugaban kasar Najeriya Buhari yayi wannan bayani.

Ba za mu bari wata kasa ta rika yi mana katsalandan ba – Najeriya ta fadawa Amurka

Buhari ya maidawa Amurka da Turai kakkausan martani kan taba CJN
Source: Facebook

Gwamnatin tarayya tayi wannan bayani ne jiya ta bakin Garba Shehu, wanda ke magana da yawun bakin shugaban kasar. Shehu ya maida martani ne ga kasar Amurka da kungiyar EU ta kasashen Turai kan jawaban da su ka fitar.

Kasashen na ketare sun nuna rashin jin dadin su game da dakatar da babban Alkalin Najeriya Walter Onnoghen da aka yi daga kan kujerar sa wanda su ke zargin hakan na iya yin tasiri a babban zaben kasar da za ayi kwanan nan.

Malam Garba Shehu ya maidawa kasashen martani yana mai cewa gwamnatin Buhari ba ta na’am da yunkurin da aka yi na jefa Najeriya cikin wani hali na dar-dar da kuma duk wani aiki da zai iya jefa zaben Najeriyar cikin hadari.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon ziyarar Shugaba Buhari a Jihar Osun

Shugaba Buhari ya kuma tabbatar da cewa babu bukatar kasashen waje su rika shiga cikin sha’anin da bai shafe su ba a Najeriya. Buhari ya kara da cewa ya na da tabbacin cewa hukumar zaben kasar za tayi aikin ta yadda ya kamata.

Shugaban kasar ya kara da cewa yana nan a kan bakar sa na cewa za ayi gaskiya da gaskiya a zaben bana. Buhari ya kuma ja-kunnen masu neman tada fitina a kasar ko daga waje cewa jami’an tsaro sun shirya tsaf domin maganin su.

Kasar Amurka da kuma kungiyar EU ta kasashen kasar Turai dai sun yi magana bayan an dakatar da babban Alkalin Najeriya. Kwanaki ma dai kasar tayi barazanar hukunta masu shirin magudi a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel