2019: Manyan zaben wasu Jihohin da jama’a su ke sa ran gani

2019: Manyan zaben wasu Jihohin da jama’a su ke sa ran gani

Saura kusan kwanaki 20 rak a fara zabe a Najeriya inda wasu Gwamnoni ke neman komawa mulki ko kuma kakaba mutanen su a kan karaga. Mun kawo maku jerin wasu jihohin da ake sa rai za a gwabza da kyau a zaben na bana.

2019: Manyan zaben wasu Jihohin da jama’a su ke sa ran gani

Akwai wasu Jihohin da jama'a su kagara su ji yadda za a kaya a zaben 2019
Source: Depositphotos

Babu wani tsari da aka bi wajen jeranta wadannan jihohi:

1. Imo

Zaben jihar Imo yana cikin wanda kowa zai so ya ga yadda za a kaya, yanzu dai jihar na hannun gwamnan APC Rochas Okorocha mai shirin barin gado, wanda ya kuma tsaida ‘dan takarar sa a wata jam’iyyar adawa bayan APC ta hana sa tikiti.

2. Kano

Jama’a da dama sun kosa su ji yadda zaben jihar Kano na bana, zai kasance inda za a fafata tsakanin gwamna mai-ci Abdullahi Ganduje da mutanen tsohon Mai gidan sa Rabiu Kwankwaso da jam’iyyar adawa ta PDP ta hannun 'dan takara Abba Yusuf.

3. Kaduna

Jihar Kaduna na cikin zaben da jama’a su ka kagara su gani a zaben na bana. Gwamna Nasir El-Rufai na neman komawa kan kujerar sa a APC tare da Abokiyar takara mace. PDP kuma ta sha alwashin karbe jihar da ta saba mulki ta hannun ‘dan takarar ta Ashiru Kudan.

KU KARANTA: Ayyuka 19 da Buhari ya bada umurnin a fara su cikin gaggawa

4. Kwara

Idanun jama’a ya karkata zuwa zaben jihar Kwara inda PDP da jam’iyyar APC za su kara da kyau. APC ta sha alwashin karbe jihar daga hannun Sanata Bukola Saraki wanda jigo ne a siyasar kasar nan kuma wanda ake ganin su ke rike da Kwara tun fil azal.

5. Ogun

Wata jihar da kuma mutane za su so ganin yadda abubuwa za su kasance ita ce Ogun inda aka samu sabani a APC bayan APC ta hana wanda gwamna Ibekunle Amosun yake so tikiti. Wannan ya sa mutanen gwamnan jihar su ka sauya sheka.

6. Zamfara

APC ta na fama da rikicin cikin gida a Zamfara, sai dai a jihar Zamfara ba a samu sauyin-sheka kamar yadda aka gani a Ogun da Zamfara ba domin har yanzu gwamnan da mutanen sa da ‘yan tawagar G8 masu adawa su na cikin jam’iyyar APC.

7. Akwa Ibom

Wani zabe da zai yi zafi a 2019 shi ne na jihar Akwa Ibom. A karon farko tun 1999, PDP tana fuskantar barazana. Gwamna Udom Emmanuel ya samu sabani da Mai gidan sa Godswill Akpabio wanda yanzu ya koma APC. Akwai kuma wasu kusoshin jihar da yanzu su na APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel