Za ayi bore idan har Shugaba Buhari bai maida Onnoghen kan kujerar sa ba

Za ayi bore idan har Shugaba Buhari bai maida Onnoghen kan kujerar sa ba

Kungiyoyi da-dam sun sa shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaba a game da sauke shugaban Alkalan Najeriya da yayi a Ranar Juma’a. Yanzu dai an huro masa wuta ya janye matakin da ya dauka.

Za ayi bore idan har Shugaba Buhari bai maida Onnoghen kan kujerar sa ba

Ana neman a sauke Tanko Mohammed daga kujerar Alkalin Alkalai
Source: Twitter

Kamar yadda mu ka ji labari, wasu kungigoyi har 46 na Matasan kasar nan sun nemi shugaban kasa Buhari ya dawo da Walter Onnoghen matsayin sa a cikin mako guda. Kungiyoyin da ke karkashin lemar YIAGA su ka bayyana wannan.

Daily Trust ta rahoto mana cewa, Darektan kungiyar nan ta YIAGA ta Matasan Afrika watau Samson Itofo yayi wani jawabi mai kaushi a Ranar Asabar inda ya nemi Buhari ya maida Walter Onnoghen a kan kujerar sa ta Alkalin Alkalai.

Itodo ya nuna cewa ba za su yadda da wannan danyen aiki da shugaban kasar yayi na sauke Walter Onnoghen tare da kuma nada Ibrahim Tanko Muhammed a matsayin Alkalin Alkalai na rikon kwarya kafin kammala shari’ar Onnoghen.

KU KARANTA: Tsagerun Neja Delta su jinjinawa Buhari a kan dakatar da Onnoghen

Sai dai wannan kungiya duk da ta nuna adawar ta ga abin da shugaban kasar yayi, ta ce ta na tare da shi wajen yaki da barna da rashin gaskiya, Sai dai Samson Itodo yace wannan ba zai sa ayi waje da babban Alkalin kasar daf da babban zabe ba.

Kafin nan dama mun ji cewa wata kungiya mai suna NIM watau Nigerian Intervention Movement ta nemi shugaba Buhari ya dawo da Walter Onnoghen kan kujerar sa nan da mako mai zuwa. NIM tace idan ba ayi hakan ba, za su yi zanga-zanga.

Babban Lauyan nan na kasa Olisa Agbakoba da kuma wani daga cikin ‘ya ‘yan Marigayi Firayim Ministan kasar nan Tafawa Balewa ne shugabannin wannan kungiya da ke neman a sauke Tanko Mohammed.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel