Duk da asarar biliyoyin daloli da yayi karkashin mulkin APC, jiya Buhari ya burge Dangote

Duk da asarar biliyoyin daloli da yayi karkashin mulkin APC, jiya Buhari ya burge Dangote

- Dangote yace sa hannun da shugaban kasa Buhari akan umarni mai lamba 007 zai bunkasa kasuwanci

- Tituna sune ginshikin kowacce cigaba don haka zasu kawo riba tare da rage asara

- Yayi kira ga gwamnati da ta gyar harajin ta yanda zata cigaba da samar da ababen more rayuwa

Duk da asarar biliyoyin daloli da yayi karkashin mulkin APC, jiya Buhari ya burge Dangote

Duk da asarar biliyoyin daloli da yayi karkashin mulkin APC, jiya Buhari ya burge Dangote
Source: Depositphotos

Babban Dan kasuwa, Aliko Dangote,yace umarnin zababbu mai lamba 007 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu a ranar juma'a zai sa kasuwanci tafiya yanda ya dace kuma yanda ake so.Babban Dan kasuwa, Aliko Dangote,yace umarnin zababbu mai lamba 007 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu a ranar juma'a zai sa kasuwanci tafiya yanda ya dace kuma yanda ake so.Babban Dan kasuwa, Aliko Dangote,yace umarnin zababbu mai lamba 007 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu a ranar juma'a zai sa kasuwanci tafiya yanda ya dace kuma yanda ake so.Babban Dan kasuwa, Aliko Dangote,yace umarnin zababbu mai lamba 007 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu a ranar juma'a zai sa kasuwanci tafiya yanda ya dace kuma yanda ake so.

Babban mai kudin Afirkan yace sabuwar dokar mai tambarin Road infrastructure development and refurbishment investment tax credit scheme zai rage yawan kudin da ake narkarwa a kasar nan don kasuwanci tare da kawo riba mai yawa.

Kungiyar Dangote na daya daga cikin kamfanoni 6 da aka zaba don kwangilar titunan tarayya 19 a sabon tsarin.

Kamfanonin zasu mori harajin bashi don gyara titunan mabudan tattalin arziki.

Da yayi magana da manema labarai a ranara juma'a bayan bikin murnar sa hannun, Dangote yace abubuwan da titunan zasu kawo masu yawa ne saboda "a yanzu da muke magana kunsan mummunan halin da titunan Najeriya keep ciki."

GA WANNAN: Duk wanda ya sake murdiyya a zabe, zai fuskanci takunkumai daga Turawan Yamma

"Wannan umarnin zai sa duk bangarorin da ba na gwamnati ba suyi amfani da jarin su, abinda suka sani da kuma kwarewar su don ganin sunyi titunan akan lokaci."

"Ba zai zamo kasuwanci ba kamar yanda aka saba, idan aka duba titin Abuja zuwa Lokoja da aka fara tun lokacin mulkin Obasanjo har yanzu ana yin shi, zai yuwu kuma ya kai nan da shekaru 5 anayi saboda kasafin kashe kudin shi uku," inji shi.

Dangote yace a sabon cigaban, gwamnatin Najeriya zata adana biliyoyin Nairori.

"A yanzu da muke magana, me kuke tunanin ya faru a misali da gwamnati take yin titin Apapa zuwa Oshodi zuwa Oworonshoki da Ojota? Wadannan titunan zasu tseratar da biliyoyin mutane da biliyoyin nairori. Bansan asarar da wasu kamfanoni suka yi ba amma ina tunanin mu bayan asarar wani kaso na ribar mu, mun rasa sama da Naira biliyan 20 a shekarar da ta gabat saboda mun kasa kwashe kayan mu daga tashar jirgin ruwa," inji shi.

Dangote yace wannan dokar zata sa kamfanoni suyi saurin zuwa da kuma gyara titituna, yanzu zaka ga motocin daukar kaya sun mamaye Legas. Hakan zai taimaka sosai. Hakan zai taimakawa masu ababen Hawa dake amfani da titunan.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel