Abin tausayi: Wani direba da ya yi tatul da giya ya afkawa masallata 4, ya kashe su har lahira

Abin tausayi: Wani direba da ya yi tatul da giya ya afkawa masallata 4, ya kashe su har lahira

A daren jiya Juma'a ne wani direba da ya yi tatul da giya ya markade wasu musulmi hudu da ke sallah a Moshood Abiola way da ke garin Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Mutane hudu da ke cikin motar su ma sun jikkata sakamakon hatsarin.

Wani da abin ya faru a gabansa ya ce direban ya dako wasu mutane uku ne cikin motarsa har da mace guda daya amma sai motar da kubce masa ya afkawa mutane da ke sallah.

Shugaban Hukumar da ke Kula da bin dokokin hanya na TRACE a Abeokuta, Olaleye Babajide ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Direba ya fadawa masallata hudu ya kashe su har lahira

Direba ya fadawa masallata hudu ya kashe su har lahira
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Jirgin kasa: Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari

Ya ce hatsarin motar ya afku ne misalin karfe 10.30 na daren Juma'a.

Ya ce, "Motar da sauka daga titi, ta bige falwaya na lantarki sannan ta afkawa wasu mutane da ke sallah a gaban masallacin Rahamot Lahill Quareeb da ke gefen titin inda nan take suka mutu."

Jami'in ya ce mammatan suna hutawa ne a gaban masallacin inda suke shirin sallar dare kafin hatsarin ya afku.

"Hatsarin ya yi muni ta yadda sai da akayi amfani da gatari sannan aka ciro direban da fasinjoji uku da ke cikin motar," inji shi.

Mr Babajide ya ce dukkan mutane uku da ke motar har da direban duk sunyi tatul da giya.

"Gudu fiye da kima da direban keyi ne ya janyo hatsarin. An samu giya da tramadol a cikin motar," inji shi.

Ya ce an kai gawarwakin wadanda suka rasu zuwa asibitin tarayya da ke Abeokuta.

Ya kuma ce biyu daga cikin wadanda ke motar sunyi yunkurin tserewa daga wurin amma an kama su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel