Dakatar da Onnoghen: Tsagerun Neja Delta sun yiwa Buhari jinjina

Dakatar da Onnoghen: Tsagerun Neja Delta sun yiwa Buhari jinjina

Kungiyar Tubabbun Tsagerun Neja Delta (RNDA) ta jinjinawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa matakin da ya dauka na dakatar da Walter Onnoghen a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya (CJN).

A cewar kungiyar, Onnoghen ya 'fadi jarrabawar nagarta.'

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Onnoghen ne a ranar Juma'a kuma ya maye gurbinsa da Justice Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin mukadashi.

Dakatar da Onnoghen: Tsagerun Neja Delta sun yiwa Buhari jinjina

Dakatar da Onnoghen: Tsagerun Neja Delta sun yiwa Buhari jinjina
Source: Twitter

A cewar shugaba Muhammadu Buhari, ya dakatar da Onnoghen ne sakamakon umurnin da ya samu daga Kotun Da'ar Ma'aikata na kasa (CCT) da ke shari'a a kan CJN din kafin a dakatar da shi bisa zarginsa da kin bayyana wasu kadarorinsa.

DUBA WANNAN: Zaben fidda gwani: Na yafewa APC - Gwamna Yari

Sanarwar da ta fito daga bakin shugaban kungiyar, Johnmark Ezonebi a ranar Asabar ta ce yabawa shugaban kasa bisa matakin da ya dauka.

Wani bangare na sanarwar ya ce: "A matsayin mu na kungiya da ke kokarin kawo cigaba a yankin mu, muna jinjina ga Shugaba Muhammadu Buhari saboda matakin da ya dauka na dakatar da CJN na kasa Mr Onnoghen ya fadi jarrabawar nagarta kuma bashi da jarumtar yaki da rashawa tun lokacin da Buhari ya nada shi a 2015.

"Kungiyar ta kuma yabawa gwamnatin tarayya saboda fara karatu a Nigerian Maritime University da ke Okerenkoko da kuma fara yashe rafin Escravos da ke Warri a kan kudi N13 biliyan wanda hakan zai bayar da dama a rika sauke kayayaki daga kasashen ketare a Warri wadda hakan zai bunkasa kasuwanci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel