Qarya ne, babu wani sabon harin makiyaya da ya kashe mutane 15 - Soji

Qarya ne, babu wani sabon harin makiyaya da ya kashe mutane 15 - Soji

- Shugaban OPWS ya karyata rahoto da kafafen yada labarai suke akan harin da makiyaya suka kai jihar Benue

- Ana yada cewa makiyaya sun kai hari a garin Makurdi har yayi sanadin rayuaka 15

- Shugaban ya bukaci yan jihar su kwantar da hankalin su tare da watsi da jita jitan

Qarya ne, babu wani sabon harin makiyaya da ya kashe mutane 15 - Soji

Qarya ne, babu wani sabon harin makiyaya da ya kashe mutane 15 - Soji
Source: Facebook

Manjo janar Adeyemi Yekini, kwamandan OPWS ya karyata rahoton kafafen yada labarai na cewa mikiyaya sun kashe yan jihar Benue 15 a sabon harin da suka kai wa yankin a jihar.

Yekini, wanda ya karyata rahoton a wata takarda da yasa hannu a ranar asabar a garin Makurdi, yace babu wadannan kashe kashen a jihar.

"Hedkwatar OPWS, tana sanar da jihar cewa jami'an tsaro basu sami rahoton kashe ko mutum daya ba ko rauni da makiyaya sukayi wa mutane a wani bangaren jihar ta Benue a watanni 7 da suka gabata. OPWS suna da rundunoni a duk yankunan jihar da ya hada da Makurdi don haka babu yanda za'ayi mutane 15 su rasa rayukan su ba tare da sanin rundunonin ba."

"Da abin ya faru da ya jawo babbar tashin tashina a garin wanda yasan yan jarida zasu dauka a yayin da suke faruwa. Akwai kuma jami'an tsaro a kasa wadanda suka hada da da mafarauta, yan sanda da jami'an DSS wadanda zasu kawo rahoto da abin ya faru ta hanyoyi daban daban."

"Hedkwatar OPWS na bukatar mutanen jihar Benue da suyi watsi da duk labarai kuma su cigaba da aiyukan su da kasuwancin su ba tare da tsoro ba, akwai tabbaci daga OPWS cewa suna shirye tsaf don kawo zaman lafiya mai dorewa a jihar Benue."

GA WANNAN: Tsugunne bata qare ba, inji NLC, duk da cewa manyan Janar din Najeriya sun tantance

Ofishin dillancin labarai ya tunatar cewa kwamandan OPWS ya sanar da manema labarai a watan Yuli 2018 cewa an kara jami'an tsaro a wuraren da abin ya shafa kuma a lokacin ana taimaka musu don komawa gidajen su.

"OPWS ta samu cika wajibcin ta ta hanyar kawo karshe ga kashe kashen da kungiyoyi masu makamai ke yi. Hukumar a yanzu ta maida hankali ne wajen tarwatsa ragowar sansanin yan ta'addan da za a iya samu a wasu bangarorin jihar Benue, Nasarawa da Taraba tare da kokarin maida yan gudun hijira gidajen su."

Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa jami'ai na musamman da suka hada da sojojin sama, sojojin kasa, sojojin ruwa, DSS da kungiyoyin leken asiri wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hada don murkushe hare haren yan ta'adda akan mutanen jihohin uku.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel