Mu taru mu kori shugaba Buhari a watan Mayu - Olu Falae

Mu taru mu kori shugaba Buhari a watan Mayu - Olu Falae

- Falae ya bukaci yan Nigeria su hada kai su tumbuke mulkin buhari

- Yace ‘yan Nigeria basa son buhari yayi tazarce

- Yace buhari kansa baisan halin da kasa take ciki ba

Mu taru mu kori shugaba Buhari a watan Mayu - Olu Falae

Mu taru mu kori shugaba Buhari a watan Mayu - Olu Falae
Source: Depositphotos

Shugaban jamiyar SDP Olu Falae ya bukaci yan Nigeria dasu hada hannu wajen kayarda mulkin buhari a zabe me zuwa. Falae ya fadi hakan ne a lokacin da Titi Abubakar matar dan takarar shugaban jamiyar PDP alhaji Atiku Abubakar ta kai ziyarar neman goyon baya ga shugabannin yarabawa na pan African social political group.

Falae ya kara da cewa a bayyana yake cewar yan Nigeria basa jin dadin mulkin Buhari saboda dole a hada dai domin ganin an kwace mulki daga hannun sa.

GA WANNAN: Duk wanda ya sake murdiyya a zabe, zai fuskanci takunkumai daga Turawan Yamma

Falae din dai ya kara cewa shi kansa buhari fa bai san halin da kasar take ciki ba kuma wasu makusantansa suna buya a rigar mulki suna aikata laifuffuka wanda shi buharin bai sani ba. Saboda haka idan ma sun kwace mulkin taimakon sa sukayi domin lokaci yayi da ya dace yaje gida ya huta. Falae ya kara bayyana cewa manufofin sa da atiku iri dayane saboda haka suna yi mishi fatan alkairi.

Jamiyar SDP dai itace wadda Jerry Gana da Donald Duke suke a matsayin yan takarar shugabancin kasa da mataimaki na jam'iyar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel