Cikakken bayani kan N27,000 da N30,000 na karin albashi - Ministan kwadago

Cikakken bayani kan N27,000 da N30,000 na karin albashi - Ministan kwadago

- Mr Chris Ngige, ministan kwadago da daukar aiki ya ce karin mafi karancin albashi na ma'aikatan kasar daga N18,000 zuwa N27,000 ya kai makura wajen cancanta

- Ya ce gwamnatin tarayya ta yanke shawarar biyan ma'aikatanta N30,000 ne domin nuna adalci da kuma jin kai ga ma'aikatan da ke aiki a ma'aikatun gwamnatin tarayyar

- Ministan ya yi kira ga daukacin al'umma da ke da ra'ayi a sabuwar dokar sabunta albashin da su gabatar da ra'ayoyin a ranar sauraron ra'ayoyi kan dokar gaban majalisar tarayya

Mr Chris Ngige, ministan kwadago da daukar aiki ya ce karin mafi karancin albashi na ma'aikatan kasar daga N18,000 zuwa N27,000 ya kai makura wajen cancanta, amma cikin adalci na gwamnatin tarayya, ta ce zata rinka biyan ma'aikatan gwamnatin tarayya N30,000 a matsayin mafi karancin albashinsu.

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Iliya Rhoda, mataimakin dartan watsa labarai na ma'aikatar da ke Abuja, wacce aka rabawa manema labarai a safiyar ranar Asabar.

A cewar ministan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti da zai nazari kan karin mafi karancin albashi a cikin watan Nuwamba 2017, inda kuma daga karshe kwamitin ya gabatar da rahotonsa da kuma bukatunsa gaban shugaban kasar.

KARANTA WANNAN: Iyaye mata kuyi hattara: An gano sinadarai masu guba a cikin nafkin din yara

Daga karshe: Ngige ya yi karin haske kan N27000 da N30,000 na karin albashi

Daga karshe: Ngige ya yi karin haske kan N27000 da N30,000 na karin albashi
Source: Depositphotos

"Domin cimma sakamako mai kyau, an kafa kwamitin ne domin yin nazari kan karin mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar, wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki daga kungiyar kwararru kan kasuwanci, masana'antu, ma'adanai da kuma noma (NACCIMA).

"Kungiyar masu samar da kayayyaki ta Nigeria (MAN), kungiyar kanana da matsakaitun masa'antu ta kasa (NASME) da kuma kungiyar tuntuba ta masu daukar aiki ta kasa (NECA)."

Ya ce N27,000 da gwamnatin tarayya ta ayyana a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar, ya shafi kowanne bangare na aiki walau aikin gwamnati ko ma'aikatu masu zaman kansu, kuma yana kunshe a cikin sabuwar dokar albashi mafi karanci na kasar.

"Gwamnatin tarayya ta dauki matakin kara yawan albashi mafi karanci na ma'aikatan da ke aiki a ma'aikatun gwamnatin tarayya daga N27,000 zuwa N30,000 wanda zai kasance albashi ma'aikaci mafi karanci mukami, a kowanne wata."

Ministan sai ya yi kira ga kungiyoyi daban daban da ke da ra'ayi kan bayanan da ke kunshe a cikin sabuwar dokar sake fasalin albashi mafi karanci na kasar na 2019 da tuni aka gabatar da shi gaban majalisar tarayya kuma ya wuce karatu na biyu da su bayyana ra'ayinsu a zaman jin ra'ayin jama'a da za a gudanar nan gaba akan sabuwar dokar albashin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel