Zabe: Buhari zai yi nasara domin haka Allah ya hukunta - Akpabio

Zabe: Buhari zai yi nasara domin haka Allah ya hukunta - Akpabio

- Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya ce Allah ya riga ya kaddara cewa Buhari ne zai yi nasara a zaben 2019

- Akpabio wanda shine jagoran Kungiyar PSC na kasa ya fadi hakan ne a taron rantsar da jagororin kungiyar na reshen Kudu maso Yamma

- Akpabio ya ce kungiyar ta yiwa Shugaba Muhammadu Buhari alkawarin kuri'u a kalla miliyan 10

Zabe: Nasarar Buhari daga Allah ne - Akpabio

Zabe: Nasarar Buhari daga Allah ne - Akpabio
Source: Facebook

Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar tarayya, Godswill Akpabio ya ce Allah ne ya kaddara nasarar Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo a babban zaben da ke tafe a watan Fabrairu.

Mr Akpabio ya yi wannan furucin ne a garin Ibadan yayin kaddamar da jagororin Kwamitin tallafawa shugaban kasa, PSC na jihar Oyo da yankin Kudu maso Yamma.

DUBA WANNAN: Zaben fidda gwani: Na yafewa APC - Gwamna Yari

Mr Akpabio wanda shine jagoran Kwamitin tallafawa Shugaban kasar na kasa baki daya kuma tsohon gwamna ne a jihar Akwa Ibom.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa PSC Kungiya ce da aka kafa domin taimakawa wurin ganin an sake zaben shugaban kasa Buhari da dukkan sauran 'yan takarar jam'iyyar APC.

Mr Akpabio ya ce kungiyar ta yi alkawarin bawa Shugaban kasa kuri'u kimamanin miliyan 10 ko sama da haka saboda sun gane cewa shi shugaba ne mai kishin al'umma da ya mayar da hankali wurin kawo canji a kasar.

Ya ce irin nasarorin da Buhari ya samu abin kwatance ne a tarihin mulkin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel