Babbar magana: Kotu ta garkame jami'an zabe bayan kama su da karbar cin hanci

Babbar magana: Kotu ta garkame jami'an zabe bayan kama su da karbar cin hanci

- Wata kotu ta garkame wasu jami'an zabe guda biyu a gidan yari har na tsawon shekaru 7 bayan da ta kamasu dumu dumu da karbar cin hanci a zaben 2015

- Kotun mai zama a Legas, ta kama Christian Nwosu da Tijjani Bashir da laifin karbar N264.8m ($730,500) daga hannun Diezani Alison-Madueke

- Wani daga cikin ma'aikatan hukumar ta INEC, Yisa Olanrewaju Adedoyin, ya amince da karbar 70m daga cikin N264.8m a wani zama da kotun ta yi a watan Mayu, 2017

Wata kotu ta garkame wasu jami'an zabe guda biyu a gidan yari har na tsawon shekaru 7 bayan da ta kamasu dumu dumu da karbar cin hanci daga tsohuwar ministar man fetur, domin tafka magudin zaben 2015.

Kotun mai zama a Legas, ta kama Christian Nwosu da Tijjani Bashir da laifin karbar N264.8m ($730,500) daga hannun Diezani Alison-Madueke.

Alison-Madueke, wacce tsohuwar hukumar OPEC ce, kuma ta rike mukamin ministar albarkatun man fetur karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tun daga hawansa har sai da ya sha kaye a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2015.

KARANTA WANNAN: Ta hanyar amfani da katin zaben ne zamu iya kawo karshen siyasar Atiku - APC

Babbar magana: Kotu ta garkame jami'an zabe bayan kama su da karbar cin hanci

Babbar magana: Kotu ta garkame jami'an zabe bayan kama su da karbar cin hanci
Source: Depositphotos

Ta kasance ana tuhumarta da sama da fadi da makudan kudade, laifukan cin hanci da rashawa a nan Nigeria da kasashen ketare.

Da yake yanke hukunci ga masu laifin guda biyu wanda kuma suke aiki a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, mai shari'a Mohammed Idris ya ce sun aikata laifin 'cin amanar aikinsu' da kuma jawo batanci ga hukumar.

Sai dai kotu ta umurci Nwosu ya mayar da wata gonar gwamnati da wasu kadarori da ke kudancin jihar Delta da kudinsu ya kai kusan N25m da kuma tsabar kudi har N5m.

Shi kuwa Bashir, an umurce shi ya mika wata kadararsa da ke babban birnin tarayya Abuja da kudinta ya kai N27m.

Wani daga cikin ma'aikatan hukumar ta INEC, Yisa Olanrewaju Adedoyin, ya amince da karbar 70m daga cikin N264.8m a wani zama da kotun ta yi a watan Mayu, 2017.

Wannan ne ya sa kotun ta bukaci ya biya fansar N10m da kuma mayar da wata kadara ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa, INEC.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.n

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel