Ta hanyar amfani da katin zaben ne zamu iya kawo karshen siyasar Atiku - APC

Ta hanyar amfani da katin zaben ne zamu iya kawo karshen siyasar Atiku - APC

- Adams Oshiomhole ya yi kira ga 'yan Nigeria da su yi amfani da katin zabensu wajen kawo karshen wa'adin siyasar PDP da Atiku Abubakar

- Oshiomhole ya kara da cewa yafiyar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yiwa Atiku abun Allah wadai ne da kuma cin fuska

- A jawabinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da gyaran tituna, jiragen kasa da kuma wutar lantarki

Shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya yi kira ga 'yan Nigeria da su yi amfani da katin zabensu wajen kawo karshen wa'adin siyasar jam'iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Oshiomhole ya yi wannan kiran a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari; mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; jagoran APC na kasa, Sanata Bola Tinubu da kuma sauran masu ruwa da tsaki a APC suka dira a Ibadan, ranar Asabar, inda suka kaddamar da yakin zaben tazarcen Buhari.

"Za mu kashe su da katin zabenmu ba wai da bakinmu ba. Ku yi amfani da katin zabenku wajen zabar shugaban kasa Buhari a ranar 16 ga watan Gabreru 2019, hakan ne kawai zai kashe Atiku da PDP a siyasance.

KARANTA WANNAN: Neman Taimako: Hauwa Suleiman na bukatar aikin kwakwalwa domin ta rayu

Domin kawo karshen siyasar Atiku: Ku yi amfani da katin zabenku - Oshiomhole ga 'yan Nigeria

Domin kawo karshen siyasar Atiku: Ku yi amfani da katin zabenku - Oshiomhole ga 'yan Nigeria
Source: Depositphotos

Oshiomhole ya kara da cewa yafiyar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yiwa Atiku abun Allah wadai ne da kuma cin fuska, bayan da rahotanni sun bayyana cewa Atiku mai cin hanci da rashawa ne.

A jawabinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da gyaran tituna, jiragen kasa da kuma wutar lantarki.

Ya kuma yi kira ga gwamnonin shiyyar Kudu maso Yamma da su mayar da hankali a bangaren Noma, domin cimma muradin gwamnatinsa na karkatar da akalar tattalin arzikin kasar daga fetur zuwa noma.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.n

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel