Alkalan kotun koli sun kauracewa bikin rantsar da Alkalan Kotun sauraron karar zabe 250

Alkalan kotun koli sun kauracewa bikin rantsar da Alkalan Kotun sauraron karar zabe 250

Mukadashin Alkalin Alkalai na kasa, Justice Tanko Muhammad ya rantsar da Alkalai 250 na Kotun sauraron karar zabe da za suyi saurari duk wasu korafe-korafe da za su biyo bayan zaben 'Yan majalisun tarayya, Gwamnoni da 'yan majalisun jiha sai dai Alkalan Kotun Koli ba su hallarci taron ba.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Alkalai kalilan ne suka hallarci taron rantsar da Alkalan na Kotun saurarn karar zaben.

An gano cewa Alkalan suna bore ne saboda dakatar da Alkalin Alkalan kasa Walter Onnoghen a matsayin Alkalin Alkalai da shugaba Muhammadu Buhari ta yi a ranar Juma'a 25 ga watan Janairu.

Alkalai sun kauracewa bikin rantsar da Alkalan Kotun sauraron karar zabe 250

Alkalai sun kauracewa bikin rantsar da Alkalan Kotun sauraron karar zabe 250
Source: Twitter

A yayin da ya ke jawabi ga sabbin Alkalan Kotun sauraron zaben da aka rantsar da su a Kotun Koli na kasa, Mukadashin CJN ya ce fanin shari'a tana fuskanatar wani kallubale a yanzu.

DUBA WANNAN: Jirgin kasa: Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari

Mr Muhammad ya ce akwai wasu da ke shirya makarkashiya na kawo rudanni a fannin na Shari'a amma ya ce yanzu ne lokacin da ya dace Alkalan su tashi tsaye su kare mutunci da kimar fannin shari'ar.

Ya ce: "A wannan lokaci da kuke rantsuwar kama aiki a matsayin Ciyamomi da mambobin Kotun sauraron karar zabe, ina son in tunatar da ku cewa wannan rantsuwar alkawari ne tsakanin ku da Allah.

"Kazalika, rantsuwa ce ta kama aiki a matsayin ku na Alkalai da kuma tabbatar da dokar kasa a kotunan mu da kotunan zabe.

"Saboda haka, ina kira gareku ku gudanar da ayyukan da gaskiya da tsoron Allah.

"Fanin shari'a yana cikin mawuyacin hali, ya zama dole ku tashi ku kare mutuncin wannan fanin gwamnatin.

"Idan wasu suna son kawo rudani a cikin fanin shari'ar, ya kamata mu kare shi. "Idan ba mu kare shi da kan mu ba, babu wanda zai yi mana. Saboda haka hakkin mu ne kare fannin shari'ar.

"Ina taya ku murna bisa wannan nadin da akayi muku kuma ina kira gareku ku dauki shi a matsayin hidima ga kasarku."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel