Sallamar Walter Onnoghen: Saraki ya ce dukkan yan majalisa su dawo aiki ranan Talata

Sallamar Walter Onnoghen: Saraki ya ce dukkan yan majalisa su dawo aiki ranan Talata

Wata majiya karfi ta bayyana cewa yan majalisan dokokin tarayya zasu koma aiki ranan Talata domin tattaunawa kan al'amarin dakatad da Jastis Walter Onnoghen a matsayin shugaba Alkalan Najeriya.

Wannan majiya ta kara da cewa yan majalisan zasuyi wata ganawar sirri a ranan Lahadi, 27 ga watan Junairu kan wannan al'amari.

Yan majalisan sun baiwa kansu hutu ranan Alhamis zuwa ranan 19 ga watan Febrairu idan aka gudanar da zaben shugaban kasa.

Amma sun canza ra'ayinsu bayan shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Alkalin alkalai Walter Onnoghen, a ranan Juma'a.

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya siffanta wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka a matsayin kama-karya.

KU KARANTA: Sabon mukaddashin CJN ya rantsar da mambobin kwamitin sauraron kararrakin zabe 250

A bangare guda, Amurka ta yi tsokaci kan labarin dakatad da shugaban Alkalan Najeriya, Walter Nkanu Onnoghen, da shugaba Muhammadu Buhari yayi a ranan Juma'a, 25 ga watan Junairu, 2019.

Shugaba Buhari ya dakatad da Onnoghen ne bisa ga wata umurni da kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT tayi a wasikar da ta turawa shugaba Buhari.

A ranan Asabar, ofishin jakadancin Amurka dake birnin tarayya Abuja ta yi tsokaci kan maganganun da haka ya jawo na cewa abinda akayi ya sanawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel