Dakatad da Jastis Onnoghen: Amurka ta nuna damuwarta

Dakatad da Jastis Onnoghen: Amurka ta nuna damuwarta

Amurka ta yi tsokaci kan labarin dakatad da shugaban Alkalan Najeriya, Walter Nkanu Onnoghen, da shugaba Muhammadu Buhari yayi a ranan Juma'a, 25 ga watan Junairu, 2019.

Shugaba Buhari ya dakatad da Onnoghen ne bisa ga wata umurni da kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT tayi a wasikar da ta turawa shugaba Buhari.

A ranan Asabar, ofishin jakadancin Amurka dake birnin tarayya Abuja ta yi tsokaci kan maganganun da haka ya jawo na cewa abinda akayi ya sanawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

KU KARANTA: Sabon mukaddashin CJN ya rantsar da mambobin kwamitin sauraron kararrakin zabe 250

Jawabin yace: "Ofishin jakadancin Amurka ta nuna damuwarta kan matakin da bangaren zantarwa ta dauka na dakatad da shugaban Alkalai da kuma nada wani ba tare da izinin majalisar dokokin tarayya ba."

"Mun lura da soke-soke cewa wannan mataki ya sabawa doka kuma ya nuna kama karya ga bangaren shari'a."

"Muna kira ga cewa ayi kyakkyawan dubi cikin abinda ake cewa kuma a shawo kan al'amarin cikin zaman lafiya, cikin doka. Muna bukatar ayi hakan ba tare da bata lokaci ba saboda kada a samu cikas a zabe."

Wannan jawabin na zuwa ne kwanaki uku bayan kasar Amurka da Ingila tayi barazanar hana duk wanda ya kawo cikas zaben biza.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel