Yanzu Yanzu: Sabon mukaddashin CJN ya rantsar da mambobin kwamitin sauraron kararrakin zabe 250

Yanzu Yanzu: Sabon mukaddashin CJN ya rantsar da mambobin kwamitin sauraron kararrakin zabe 250

- Kasa da sa'o'i 24 bayan nadinsa, sabon mukaddashin shugaban alkalan Najeriya Ibrahim Tanko Muhammed ya yi yunkurinsa ta farko

- Muhammad a ranar Asabar, 26 ga watan Janaru ya nada tare da rantsar da mambobin kwamitin sauraron kararrakin zabe su 250

- Ya bukaci alkalan da su gudanar da ayyukansu cikin mutunci da tsoron Allah a zukatansu

Ibrahim Tanko Muhammed, sabon mukaddashin shugaban alkalan Najeriya (CJN) a ranar Asabar, 26 ga watan Janairu ya rantsar da mambobin kwamitin sauraron kararrakin zabe su 250, gidan talbijin din Channels TV ta ruwaito.

A lokacin bikin kaddamarwar da ya gudana a Abuja a ranar Asabar, Muhammed ya bukaci mambobin kwamitin sauraron kararrakin zaben da su gudanar da ayyukansu cikin mutunci da tsoron Allah a zukatansu.

Yanzu Yanzu: Sabon mukaddashin CJN ya rantsar da mambobin kwamitin sauraron kararrakin zabe 250

Yanzu Yanzu: Sabon mukaddashin CJN ya rantsar da mambobin kwamitin sauraron kararrakin zabe 250
Source: Twitter

Da farko, Legit.ng ta rahoto sabbin bayanai da suka billo kan dalilin da yasa gwamnatin tarayya ba ta jira kotu ta bayar da umurni akan tsige babban alkalin-alkalan Najeriya Walter Onnoghen ba a Abuja a ranar Asabar, 26 ga watan Janairu.

An sanya ran cewa Justice Onnoghen zai kaddamar da kwamitocin alkalai 250 da za su jagoranci gudanarwar zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: 2019: Jirgin Buhari ya isa kudu maso yamma don isar da sakon ‘Next Level’ na APC

Majiyar tace: “Adadin mambobin da za su zauna a kwamitocin zabe su 250 ne. Kwamitocin sun hada da na sauraron kararrakin zaben yan majalisar dokoki, kotun sauraron kararrakin zaben gwamna, da kuma na sauraron kararrakin zaben yan majalisar dokoki na jiha.

“Cire shi da aka yi cikin gaggawa don kokarin dakatar da taron ne ko kuma yunkurin cire sunayen wasu alkalai daga jerin sunayen. Hakan ce za ta kasance."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel