Okorocha ya caccaki kungiyar Ohanaeze kan marawa Atiku baya da suka yi

Okorocha ya caccaki kungiyar Ohanaeze kan marawa Atiku baya da suka yi

- Gwamna Rochas Okorocha ya caccaki shugabannin kungiyar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo akan hukuncin da ta yanke na marawa Atiku baya a zabe mai zuwa

- Yace kungiyar Ohanaeze ba jam’iyyar siyasa bace mai rijista sannan cewa ba ta da mazabar da za ta kawo wa PDP

- Okorocha yace duk da kungiyar bata marawa APC baya ba a 2015 hakan bai hana ta yin nasarar zabe ba

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya caccaki shugabannin kungiyar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo akan hukuncin da ta yanke kwanan nan na marawa dan takarar shugaban kasa na Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar baya a zaben watan mai zuwa.

Gwamna Okorocha, wanda ya nuna rashin jin dadi a wani jawabi daga sakataren labaransa, Sam Onwuemeodo, ya nuna cewa kungiyar Ohanaeze ba jam’iyyar siyasa bace mai rijista sannan cewa ba ta da mazabar da za ta kawo wa Atiku.

Okorocha ya caccaki kungiyar Ohanaeze kan marawa Atiku baya da suka yi

Okorocha ya caccaki kungiyar Ohanaeze kan marawa Atiku baya da suka yi
Source: Depositphotos

Gwamnan ya bayyana cewa wannan ba shine karo na farko da kungiyar yan Igbon ke marawa dan takarar shugaban kasa na PDP baya ba, inda ya tuna cewa a shekarar 2015 sun yi hakan amma duk da haka dan takararsu na shugaban kasa ya fadi zabe sannan jam’iyyar APC ta yi nasara.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dalilin da yasa Buhari yayi gaggawan sallamar shugaban Alkalin Najeriya - Sabon bincike

“Mutun zai yi tunanin Ohanaeze za ta yi taka-tsan-tsan a wannan karon biyo bayan abunda ya faru a 2015. Don haka, ya kamata ace kungiyar tayi abu na daban, musamman idan suka yi la’a kari da cewa dukkanin yan Igbo imma PDP, APC, APGA, ADC or SDP duk mambobin kungiyar Ohanaeze ne, inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel