Yanzu Yanzu: Dalilin da yasa Buhari yayi gaggawan sallamar shugaban Alkalin Najeriya - Sabon bincike

Yanzu Yanzu: Dalilin da yasa Buhari yayi gaggawan sallamar shugaban Alkalin Najeriya - Sabon bincike

- Sabbin bayanai sun billo a kan dalilin da ya sa Buhari ya gaza jiran kotu don yanke hukunci akan Shugaban Alkalan Najeriya

- Anyi hasashen cewa tsige shugaban alkalan da aka yi cikin gaggawa don kokarin dakatar da taron kaddamar da alkalan da za su yi alkalanci akan korae-korafen zabe ne ko kuma yunkurin cire sunayen wasu alkalai cikin kwamitocin

Karin bayanai sun billo a Abuja a ranar Asabar, 26 ga watan Janairu kan dalilin da ya sa Buhari ya gaza jiran kotu don yanke hukunci akan Shugaban Alkalan Najeriya.

An tattaro cewa an ba Onnoghen dokar kaddamar da alkalai da za su yi alkalanci akan gudanarwar zaben 2019 a kasar.

Dalilin da yasa Buhari yayi gaggawan sallamar shugaban Alkalin Najeriya -Bincike

Dalilin da yasa Buhari yayi gaggawan sallamar shugaban Alkalin Najeriya -Bincike
Source: UGC

Alkalin ya sanya ranar yau Asabar a matsayin ranar kaddamar da kwamitocin korafin zabe.

Bisa ga wasu majiyoyi abun dogaro jerin kwamitocin zaben watar gobe da ya kamata a rantsar a kotun koli sun kasance alkalai 250.

Majiyar tace: “Adadin mambobin da za su zauna a kwamitocin zabe su 250 ne. Kwamitocin sun hada da na sauraron kararrakin zaben yan majalisar dokoki, kotun sauraron kararrakin zaben gwamna, da kuma na sauraron kararrakin zaben yan majalisar dokoki na jiha.

KU KARANTA KUMA: 2019: Jirgin Buhari ya isa kudu maso yamma don isar da sakon ‘Next Level’ na APC

“Cire shi da aka yi cikin gaggawa don kokarin dakatar da taron ne ko kuma yunkurin cire sunayen wasu alkalai daga jerin sunayen. Hakan ce za ta kasance."

An tattaro cewa alkalan da za su kafa kwamitocin sun isa Abuja, tare da burin cewa za a kaddamar da su a ranar Asabar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel