Da duminsa: Sojin Sama sun yiwa Boko Haram luguden wuta a sansaninsu da ke Kaicungul

Da duminsa: Sojin Sama sun yiwa Boko Haram luguden wuta a sansaninsu da ke Kaicungul

- Dakarun Sojin Saman Najeriya na sunyi nasarar kai hari wani mabuyar 'yan Boko Haram da ke Kaicungul a Borno

- Sojojin sunyi amfani da jiragen yaki biyu kirar Alpha Jet inda suka yiwa mabuyar luguden wuta suka kashe 'yan ta'addan da yawa

- An hai harin ne bayan an samu bayanan sirri kuma an tabbatar da cewa wurin sansani ne na mayakan na Boko Haram

Rundunar Sojin Saman Najeriya NAF ta ce dakarunta na Operation Lafiya Dole sun lalata wani mabutar 'yan ta'adda tare da kashe wasu da dama cikinsu a Kaicungul wani gari da ke kilo mita 100 Arewa maso Yammacin Monguna a Arewacin Borno.

Sojojin Sama sun ragargaji 'yan Boko Haram a sansaninsu da ke Borno

Sojojin Sama sun ragargaji 'yan Boko Haram a sansaninsu da ke Borno
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Damu-dumu: An kama wani babban jami'in gwamnatin Jigawa yana lalata fostocin jam'iyyar adawa, hoto

Direktan watsa labarai na NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Abuja inda ya ce an kai sumamen ne a ranar Juma'a.

"An kai sumamen na bayan samun bayannan sirri da ya tabbatar cewa 'yan ta'addan na amfani da kauyen a matsayin wurin haduwa su shirya kai hari a sansanin sojoji.

"Dakarun sojin sun kai harin bayan da binciken da aka gudanar a inda aka gano din ya nuna alamun kaiwa da komowa na 'yan ta'adda a sansanin.

"An tura jiragen yaki na Alpha Jet guda biyu inda su kayi luguden wuta kuma suka lalata sansanin."

"Jiragen yakin biyu sun kai hari a daya bayan daya inda kuma dukkansu su kayi nasarar sakin bama-baman su a wuraren da 'yan ta'addar su ke inda suka lalata gine-gine da kashe wasu 'yan ta'addan," inji Daramola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel