Kamfen din Buhari Jaruman Kannywood sun fantsama jihar Kano

Kamfen din Buhari Jaruman Kannywood sun fantsama jihar Kano

- Manyan jaruman masana’arta shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sun fantsama cikin garin Kano domin tallata shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin matasa da Nasir Adhama ne ya shirya wannan gangami

- A yau Asabar ne Buhari ya bar Abuja zuwa Ibadan, babbar birnin jihar Oyo, domin ci gaba da kamfen dinsa

A ranar Juma’a 25 ga watan Janairu ne manyan jaruman masana’arta shirya fina-finan Hausa ta Kannywood suka fantsama cikin garin Kano domin tallata shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

‘Yan wasan sun sanya riguna dauke da tambarin APC, da hotunan Shugaba Muhammadu Buhari.

Kamfen din Buhari Jaruman Kannywood sun fantsama jihar Kano

Kamfen din Buhari Jaruman Kannywood sun fantsama jihar Kano
Source: UGC

Jaruman da suka halarci wannan tattaki sun hada da irin su Ali Nuhu, Alhassan Kwale, Adam Zango, Lawal Ahmed, Nuhu Abdullhi, Ibrahim Maishinku, Rabiu Rikadawa, Daushe da sauran su.

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin matasa da Nasir Adhama ne ya shirya wannan gangami.

A halin da ake ciki, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar, 26 ga watan Janairu, ya bar Abuja zuwa Ibadan, babbar birnin jihar Oyo, domin ci gaba da kamfen dinsa kwana daya bayan ya huta a ranar Juma’a, 25 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 8 da Buhari ya fadi kan Jastis Walter Onnoghen yayinda ya sallameshi

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa kafin hutun, shugaban kasa da mambobin kungiyar kamfen din jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Alhamis, 24 ga watan Janairu sun kaddamar da kudirin shugaban kasar na neman tazarce a jihohin Anambra da Enugu.

A Ibadan, shugaba Buhari zai gana da shugabannin gargajiya a sakatariyar shugabannin kafin daga nan ya garzaya wajen taron gangamin kamfen din na APC a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel