2019: Jirgin Buhari ya isa kudu maso yamma don isar da sakon ‘Next Level’ na APC

2019: Jirgin Buhari ya isa kudu maso yamma don isar da sakon ‘Next Level’ na APC

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar, 26 ga watan Janairu, ya bar Abuja zuwa Ibadan, babbar birnin jihar Oyo, don yin kamfen

- Shugaban kasa da mambobin kungiyar kamfen din APC a ranar Alhamis, 24 ga watan Janairu sun kaddamar da kudirin shugaban kasar na neman tazarce a jihohin Anambra da Enugu

-Buhari zai gana da shugabannin gargajiya a sakatariyar shugabannin kafin daga nan ya garzaya wajen taron gangamin kamfen din na APC a jihar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar, 26 ga watan Janairu, ya bar Abuja zuwa Ibadan, babbar birnin jihar Oyo, domin ci gaba da kamfen dinsa kwana daya bayan ya huta a ranar Juma’a, 25 ga watan Janairu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa kafin hutun, shugaban kasa da mambobin kungiyar kamfen din jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Alhamis, 24 ga watan Janairu sun kaddamar da kudirin shugaban kasar na neman tazarce a jihohin Anambra da Enugu.

2019: Jirgin Buhari ya isa kudu maso yamma don isar da sakon ‘Next Level’ na APC

2019: Jirgin Buhari ya isa kudu maso yamma don isar da sakon ‘Next Level’ na APC
Source: UGC

A Ibadan, shugaba Buhari zai gana da shugabannin gargajiya a sakatariyar shugabannin kafin daga nan ya garzaya wajen taron gangamin kamfen din na APC a jihar.

Ana sanya ran cewa shugaban kasar da mambobin kungiyar kamfen dinsa za su yi jawabi a wajen gangami sannan su isar da sakonnin ‘Next Level’ g mutanen jihar.

Ana kuma sanya ran Buhari zai ja jirgin kamfen dinsa zuwa Osogbo, jihar Osun duk a yau.

KU KARANTA KUMA: Jerin ayyuka 19 da Buhari ya bayar da umurnin a fara yi da gaggawa

A wani lamari na daban, Kungiyar yakin neman dan takarar shugabancin kasa na Jam'iyyar Peoples Democratic PDP ta dage kamfen din ta domin nuna kin amincewa da dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya, Justice Walter Onnoghen da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a jiya Juma'a.

Wannan dagewar ya sa jam'iyyar ba za ta gudanar da yakin neman zaben ta a jihar Benue ba a ranar Asabar kamar yadda ta shirya a baya.

An gano cewa jam'iyyar ta yanke shawarar dage yakin neman zaben ne saboda nuna "goyon bayanta ga fannin shari'a na Najeriya."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel