Jerin ayyuka 19 da Buhari ya bayar da umurnin a fara yi da gaggawa

Jerin ayyuka 19 da Buhari ya bayar da umurnin a fara yi da gaggawa

Tituna 19 masu tsawon kilomita 794.4 ne wasu kamfanoni shida za su gina sakamakon sabuwar dokar Executive Order 007 da shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a akai a ranar Juma'a 25 ga watan Janairu.

Ministan Kudi, Zainab Ahmed ta lissafa tittunan da za a gina a wurin taron rattaba hannu a kan dokar da aka gudanar a dakin taro da ke fadar Shugaban Kasa a Abuja. Ta ce an kirkiri dokar ne saboda magance matsalar rashin kyawu da isasun tituna a Najeriya.

Ta ce shirin zai kwadaitar da 'yan kasuwa su saka hannun jari a harkar gine-gine a kasar ta saboda karancin haraji da za a karba daga hannunsu. Za a gudanar da aikin ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da 'yan kasuwa.

Cikaken jerin ayyuka 19 da Buhari ya bayar da umurnin a fara yi da gaggawa

Cikaken jerin ayyuka 19 da Buhari ya bayar da umurnin a fara yi da gaggawa
Source: Twitter

A karo na farko na shirin, kamfanoni guda shida ne suka amince su shiga a dama da su, kamfanonin sun hada:

a) Dangote Industries Limited;

b) Lafarge Africa Plc;

c) Unilever Nigeria Plc;

d) Flour Mills of Nigeria Plc;

e) Nigeria LNG Limited; da

f) China Road and Bridge Corporation Nigeria Limited.

DUBA WANNAN: Jirgin kasa: Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari

Ga jerin tituna 19 da kamfanonin za su fara gina a karo na farko na shirin wadda tsawonsa ya kai kilomita 794.4 da aka za fara a jihohi 11 daga mazabun siyasa 6 na kasar nan:

1) Ginin babban titin Ashaka-Bajoga a jihar Gombe ;

2) Sake ginin titin Dikwa-GambaruNgala a jihar Borno;

3) Sake ginin titin Bama-Banki Road a jihar Borno;

4) Gyaran titin Sharada Road a jihar Kano;

5) Gyaran titin Nnamdi Azikiwe Expressway/Bypass, a jihar Kaduna;

6) Sake ginin titin Birnin Gwari Expressway – Road a jihar Kaduna;

7) Sake ginin titin Birnin Gwari – Dansadau Road a jihar Kaduna;

8) Sake ginin titin Makurdi-Yandev-Gboko a jihar Benue;

9) Sake ginin titin Zone Roundabout-House of Assembly Road a jihar Benue;

10) Sake ginin titin Obajana-Kabba Road a jihar Kogi;

11) Sake ginin titin Ekuku-Idoma-Obehira a jihar Kogi;

12) Ginin AdaviEba-Ikuehi-Obeiba-Obokore Road a jihar Kogi;

13) Gyaran titin Lokoja-Ganaja Road a jihar Kogi;

14) Ginin Ofeme Community Road Network da Gada a jihar Abia;

15) Gyaran titin Obele-Ilaro-Papalanto-Shagamu Road a jihar Ogun;

16) Sake ginin titin Sokoto Road a jihar Ogun;

17) Sake ginin titin Apapa-Oshodi-Oworonshoki-Ojota Road a jihar Legas;

18) Ginin Bodo-Bonny Road & Bridges zuwa Opobo Channel a jihar Rivers; da

19) Gyaran titin Benin City – Asaba Road a jihar Edo”.

Ministan kudi ta ce har yanzu gwamnati na cigaba da neman wasu kamfanoni masu son saka hannun jari da jihohin gwamnati da za su saka jari cikin ayyukan domin yin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel